Kotu ta yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 15 kan fataucin Hodar Iblis

Kotu ta yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 15 kan fataucin Hodar Iblis

- Kotu ta bayar da umarnin garkame wani Matashi a gidan 'Dan Kande har na tsawon shekaru 15

- An cafke wani Matashi da Hodar Iblis mai nauyin kilo daya da rabi a jihar Legas

- Hukumar hana ta'ammali da fataucin muggan kwayoyi ta NDLEA ta cafke Matashin tattare da Hodar Iblis a cikin 'yan Hanjin cikin sa

A yau Juma'a, wata babbar kotun tarayya a jihar Legas, ta zartar da hukuncin dauri na shekaru 15 a gidan kaso kan wani Matashi mai shekaru 16, Onyeka Ifobi, da laifin safara da kuma fataucin Hodar Iblis mai nauyin kilo daya da rabi.

Matashin da ake zargi ya shiga hannu a sakamakon kokari na hukumar hana ta'ammali da fataucin miyagun kwayoyi watau NDLEA, inda ta cikwikwiye kugunsa yayin dawowarsa daga kasar Brazil dauke da kayen maye.

Majiyar Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, safarar Hodar Iblis daga wata kasa zuwa Najeriya ya sabawa sashe na 11 zuwa na 14 cikin dokokin da hukumar NDLEA ta gindaya shekaru 14 da suka gabata.

Kotu ta yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 15 kan fataucin Hodar Iblis

Kotu ta yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 15 kan fataucin Hodar Iblis
Source: Depositphotos

Imaobong Iroabuchi, jami'a mai shigar da kara a gaban babbar kotun ta bayar da shaidar cewa, hukumar ta NDLEA ta yi ram da Mista Ifobi a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke birnin Legas a ranar 27 ga watan Satumba na shekarar da ta gabace mu.

Kamar yadda shafin jaridar Leadership ya ruwaito, Mista Ifobi ya hadidiye wannan muguwar Hoda ta Iblis daga kasar Brazil inda ya nufaci ketarewa ta Najeriya zuwa kasar Morocco da ke Arewacin nahiyyar Afirka.

KARANTA KUMA: 2019: Ya kamata al'ummar Najeriya su sake bai wa Buhari wata damar - Dakta Mahmood Abubakar

Lauyan wanda ake tuhuma ya roki rangwami na kotun yayin zartar da hukuncinta, inda a cewarsa baya ga nadama kuma wannan shine karo na farko da ya aikata wani mugun laifi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruuwaito cewa, kotun yayin zartar da hukuncinta ta bayyana cewa, ba bu wasu alamu na nadama a tattare da wanda ake zargi, inda ta zartar da hukuncin dauri na zama gidan 'Dan Kande har na tsawon shekaru 15 ba tare da wata tara ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel