Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin tawagar kudu maso gabas

Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin tawagar kudu maso gabas

Buhari ya karbi bakuncin tawaga kudu maso gabas da kuma al’umman Enyimba Economic City. An kuma kulla yarjejeniya tsakanin kamfanin Nigeria Special Economic Zone Investment Company Limited da Enyimba City Development Company Limited.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tawaga da shugabannin yankin kudu maso gabas da kuma al’umman Enyimba Economic City.

Buhari ya kuma shaida kulla yarjejeniya tsakanin kamfanin Nigeria Special Economic Zone Investment Company Limited da Enyimba City Development Company Limited a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a, 7 ga watan Disamba.

Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin tawagar kudu maso gabas (hoto)

Yanzu Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin tawagar kudu maso gabas
Source: Facebook

Wadanda suka halarci wajen sun hada da Mista Wale Edun, kwamishinan fili da birane Barista Uche Ihediwa, da kuma Mista Darl Uzu shugaban tawagar.

Haka zalika gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele tare da babban mai ba gwamnatin jihar Abia shawara, Mista Sam Hart sun kasance a wajen.

KU KARANTA KUMA: Dokar zabe: Ku bi ta kan Shugaba Buhari – PDP ga majalisar dokokin kasar

A wani lamari na daban, mun ji cewa Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Demcoratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya yi mumunan raddi ga shugaba Buhari kan rashin rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe.

Atiku ya nuna bacin ransa kan wannan abu da shugaba yayi kuma ya nuna shakku kan maganar Buhari cewa zai gudanar da zaben 2019 cikin gaskiya da amana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel