2019: Ya kamata al'ummar Najeriya su sake bai wa Buhari wata damar - Dakta Mahmood Abubakar

2019: Ya kamata al'ummar Najeriya su sake bai wa Buhari wata damar - Dakta Mahmood Abubakar

- Rikon sakainar kashin na gwamnatocin baya ya haddasawa shugaba Buhari cikas wajen jagorantar Najeriya

- Shugaban tsare-tsare na kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari ya ce Buhari zai inganta kasar nan muddin aka sake ba shi wata damar

- Dakta Mahmood ya nemi al'ummar Najeriya da su sake sanya amincin su akan shugaban kasa Buhari

A yau Juma'a shugaban gudanar da tsare-tsare na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dakta Mahmood Abubakar, ya kirayi al'ummar Najeriya kan sake bai wa ubangidansa dama da cewarsa al'amurra za su inganta a kasar nan.

Jagoran kungiyar, ya nemi al'ummar Najeriya kan sake goyon bayan shugaban kasa Buhari yayin babban zabe na 2019 domin kuwa yana da yakinin cewa al'amurra za su inganta a kasar nan muddin ya cimma nasara.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Dakta Abubakar ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da sabon reshen kungiyar ta goyon bayan shugaba Buhari na Kudu maso Yammacin kasar nan a birnin Ibadan na jihar Oyo.

2019: Ya kamata al'ummar Najeriya su sake bai wa Buhari wata damar - Dakta Mahmood Abubakar

2019: Ya kamata al'ummar Najeriya su sake bai wa Buhari wata damar - Dakta Mahmood Abubakar
Source: Depositphotos

A cewarsa, gwamnatin shugaba Buhari ta yi kacibus da matsaloli gami da fuskantar kalubalai sakamakon arangama da kuma cin gajiyar al'amurra na rikon sakainar kashi da gwamnatocin baya ta yiwa kasar nan.

Sai dai ko shakka ba bu Dakta Abubakar ya kyautata zaton sa gami da sa ran cewa shugaba Buhari zai ingantawa al'ummar kasar matukar sun sake ba shi wata dama ta bayyana goyon bayan su a gare shi yayin babban zaben kasa na 2019.

KARANTA KUMA: Jami'ar Ebonyi ta sallami Malamai da Ma'aikata 63 da laifukan cin zarafi da keta haddi

Ya kara da cewa, matsaloli gami da kalubalai da shugaba Buhari ya taras yayin cin gajiyar mulkin kasar nan musamman matsi na tattalin arziki da ya auku tun a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya sanya gwamnatin sa ta samu cikas da tangarda wajen cimma burikan da ta kudirta.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar kabilar Ibo ta haramtawa Inyamurai mazauna jihohi 19 na Arewacin Najeriya komawa Mahaifar su domin kada kuri'unsu yayin zaben kasa na badi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel