Kashedin gwamnonin APC da Oshiomhole ya baqantawa ya sake razana jam'iyyar APC

Kashedin gwamnonin APC da Oshiomhole ya baqantawa ya sake razana jam'iyyar APC

- Jam'iyar APC ta shiga damuwa a bisa hukuncin wasu mambobin ta da aka qwara

- Oshiomhole yace jam'iyar itace zata lashe zaben gwamna a jihar Imo da Ogun

- Gwamnan jihar Imo ya bawa sirinkin sa damar siyan form din takara a wata jam'iyar

Kashedin gwamnonin APC da Oshiomhole ya baqantawa ya sake razana jam'iyyar APC

Kashedin gwamnonin APC da Oshiomhole ya baqantawa ya sake razana jam'iyyar APC
Source: Facebook

Jam'iyar APC tana cikin damuwa a bisa dalilin hukuncin da wasu mambobin ta da aka qwara suka dauka wanda ya hada da gwamnan jihar Ogun Ibukunle Amason da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha wadanda aka hana damar kara tsayawa takara a jihohin su.

Banda wadannan gwamnoni guda Biyu akwai wasu mambobi da jam'iyar ta hana takara wadanda a halin yanzu basa goyan bayan ta.

A ranar Laraba ciyaman na jam'iyar Adam Oshiomhole yace jam'iyar ta APC ce zata lashe zaben jihar Imo da Ogun koda babu goyan bayan Amason da Okorocha.

DUBA WANNAN: Gara zaman talauci a gida da rayuwar wulakanci a bauta, balle fa nutsewa a yashi ko teku

Banda wannan furuci na Oshiomhole wasu mambobin jam'iyar suna tunanin wadanda aka qwara zasu iya lalatawa jam'iyar damar da take da iya.

Amason, Okorocha da Abdulazeez Yari sune wadanda jam'iyar ta hana 'yan takarar su dama.

Sannan gwamnan jihar Imo ya bawa sirikin sa damar yace ya siyi tikitin tsayawa takara a wata jam'iyar inda shi kuma yake cikin jam'iyar APC inda yake neman kujerar Sanata.

Yayin da shi kuma gwamnan jihar Ogun yace yana baya jam'iyar a bangaren shugaban cin kasar amma a bangaren gwamna baya goyan bayan jam'iyar.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel