Dokar zabe: Ku bi ta kan Shugaba Buhari – PDP ga majalisar dokokin kasar

Dokar zabe: Ku bi ta kan Shugaba Buhari – PDP ga majalisar dokokin kasar

Sakamakon kin sanya hannu a gyararen dokar zabe da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai yi ba, kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bukaci majalisar dokokin kasar da su ceci damokradiyyar kasar ta hanyar bi ta kan shugaban kasar ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bukaci majalisar dokokin kasar da su ceci damokradiyyar kasar ta hanyar bi ta kan shugaban kasar ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyar kamfen din PDP din ta bayyana a wata sanarwa da ta saki a ranar Juma’a, 7 ga watan Disamba ta hannun Kola Ologbondiyan, babban daraktan labaran kungiyar, cewa akwai bukatar yan majalisar su dauki mataki tunda hukuncin shugaban kasar yunkuri ne na garkuwa da kasar, da kuma haddasa rikici a tsarin zabe da kuma tarwatsa yadda za’a gudanar da zaben 2019, ganin cewa babu ta yadda zai yi nasara idan har aka yi zabe na gaskiya.

Dokar zabe: Ku bi ta kan Shugaba Buhari – PDP ga majalisar dokokin kasar

Dokar zabe: Ku bi ta kan Shugaba Buhari – PDP ga majalisar dokokin kasar
Source: Depositphotos

Ta kuma bayyana cewa kin sanya hannu a dokar da shugaban kasar ya ki yi lokuta da daman a iya haifar da magudin zabe da kuma haifar da rashin kwanciyar hankali a siyasa da kuma rikici, wanda ka iya zama barazana ga damokradiyyar kasar.

Kungiyar ta kuma gayyaci yan Najeriya das u lura cewa wannan shine karo na hudu da shugaba Buhari na kin sanya hannu a dokar zaben, ba tare da wani kwakwaran dalili bat un bayan da yan Najeriya suka dawo daga rakiyan shi.

Yayinda suka bukaci majalisar dokoki da ta ceto damokradiyyar kasar, kungiyar ta kuma yi kira ga dukkanin jam’iyyun siyasa, masu fada aji da yan Najeriya bakii daya da su tashi tsaye domin makomar kasarsu da kuma tabbatar da ganin anyi zabe na gaskiya da amana.

KU KARANTA KUMA: Majalisar Dinkin Duniya ta janye ma’aikata daga Rann yayinda Boko Haram suka kai hari sansanin yan gudun hijira

A baya mun ji cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi watsi da dokar zabe ne saboda yana iya kawo cikas ga zaben 2019.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin kasar.

A wasikar an tattaro cewa shugaban kasar ya ce sanya hannu a dokar zaben na iya haifar da rashin gaskiya da rudani a zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel