An nemi Gwamnonin Jam'iyyar APC an rasa wajen babban taron NEC

An nemi Gwamnonin Jam'iyyar APC an rasa wajen babban taron NEC

Labari ya zo mana cewa da-dama daga cikin Gwamnonin Jihohi na Jam'iyyar APC ba su halarci taron Jam’iyyar da Adams Oshiomhole ya shirya ba. An yi taron ne a jiya Alhamis 7 ga Watan Disamban nan.

An nemi Gwamnonin Jam'iyyar APC an rasa wajen babban taron NEC

Mafi yawan Gwamnonin Jam'iyyar APC sun tuburewa Oshimhole
Source: Facebook

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya shirya taro na Majalisar NEC inda ya sa rai cewa Gwamnoni APC akalla 9 da kuma ‘Yan takarar Gwamna 20 na Jam’iyyar za su halarta. Sai dai kuma da-dama ba su zo ba.

Gwamnonin Jihohi 2 ne kacal su ka halarci wannan babban taro da aka yi. Gwamnonin su ne: Abubakar Sani Bello na Jihar Neja da kuma Takwaran sa na Jihar Filato Simon Lalong. An yi akalla awa 2 ana wannan zama a cikin Abuja.

KU KARANTA: Gwamna Okorocha ya raba kan APC gida 2 saboda takarar Surukin sa

Lanre Isa-Onilu, wanda shi ne yake magana da yawun bakin Jam’iyyar ta APC mai mulki, yayi gum game da lamarin bayan ‘Yan jarida sun tuntube sa a wayar salula game da rashin halartar taron da aka samu daga Gwamnonin Jihohi.

A taron dai Jam’iyyar tayi kira ga ‘Yan takarar ta na Gwamnoni da su guji abin da zai jawo rikici wajen yakin neman zabe. Jam’iyyar ta kuma shirya wannan taro ne domin ‘Yan takarar ta da aka ba tuta a Jihoji dabam-dabam su san junan su.

Yanzu haka dai wasu Gwamnoni wanda su ka hada da Abdulaziz Yari, Ibikunle Amosun da kuma Rochas Okorocha su na rikici da Shugaban APC. A halin yanzu kuma dai lokacin canza sunayen ‘Yan takara ya kure balle ayi wani sulhu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel