Atiku da jam'iyyu 41 sun gana a garin Abuja kan shirye-shiryen Zaben 2019

Atiku da jam'iyyu 41 sun gana a garin Abuja kan shirye-shiryen Zaben 2019

- Atiku na ganawa da kungiyar hadin kan jam'iyyu ta CUPP a garin Abuja

- Kungiyar ta bayyana amincinta na goyon baya ga Atiku yayin zaben 2019

- Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi kira kan tabbatar da zabe na gaskiya da adalci

Mun samu cewa rahoton, a halin yanzu cikin babban birnin kasar nan na tarayya, kungiyar hadin kai ta jam'iyyu watau Coalition of United Political Parties, CUPP, na gudanar taron gaggawa tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa, ganawar na gudana ne a babban Otel din Transcorp Hilton da ke garin Abuja domin tattaunawa da kuma shimfidar tsare-tsare gami da daura damara yayin gabatowar babban zabe na 2019.

Atiku da jam'iyyu 41 na ganawa a garin Abuja kan shirye-shiryen Zaben 2019

Atiku da jam'iyyu 41 na ganawa a garin Abuja kan shirye-shiryen Zaben 2019
Source: Twitter

Shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, yayin gabatar da jawabansa ya bayyana cewa, tabbatuwa ta gudanar zabe mai inganci shine nauyi da rataya a wuyan dukkanin jam'iyyu da ke karkashin kungiyar ta CUPP.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan ganawa na gudana ne bayan kwana guda da kungiyar CUPP ta bayyana aminci gami da goyon baya ga Atiku a matsayin dan takararta yayin babban zabe na badi.

KARANTA KUMA: An haramtawa Inyamurai Mazauna Arewa komawa Mahaifarsu yayin Zaben 2019

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Larabar da ta gabata kungiyar CUPP ta kunshin jam'iyyu 41 ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rattaba hannu kan sabuwar doka ta gyara salon aiwatar da zabe a kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa babban Bankin nan na ci gaban nahiyyar Afirka watau AFDB, za ya narka makudan kudi na N258m wajen aiwatar da muhimman ayyuka a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel