Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi watsi da dokar zabe da aka gyara

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi watsi da dokar zabe da aka gyara

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da dokar zabe da aka gyara

- Hadimin shugaban kasa akan harkokin majalisar dokoki ne ya sanar da matsayar shugaban kasa

- Enang ya ce shugaban kasar ya amince da gyararren dokar hukumar makarantun jami’a na kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da gyararren dokar zabe.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Ita Enang, babban mataimakin shugaban kasa akan harkokin majalisar dokoki (majalisar dattawa) ne ya sanar da matsayar shugaban kasa a ranar Juma’a, 7 ga watan Disamba.

Ya ce shugaban kasar ya sanar wa da majalisar dokokin kasar hukuncin sa.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi watsi da dokar zabe da aka gyara

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi watsi da dokar zabe da aka gyara
Source: Depositphotos

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi watsi da dokar zabe ne saboda yana iya kawo cikas ga zaben 2019.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin kasar.

A wasikar an tattaro cewa shugaban kasar ya ce sanya hannu a dokar zaben na iya haifar da rashin gaskiya da rudani a zabe mai zuwa.

Shugaba Buhari ya kuma roki yan majalisan da su sake duba wasu rukuni na dokar, inda ya ba da yakinin cewa hakan zai fara aiki bayan zabe.

Sai dai kuma Enang ya ce shugaban kasar ya amince da gyararren dokar hukumar makarantun jami’a na kasa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari za ta kaddamar da fara aikin wasu manyan madatsan ruwa guda 7

Majalisar dokokin kasar ta gabatar da dokar ne a watan Yuli sannan aka mika ga shugaban kasa a ranar 3 ga watan Agusta.

Shugaban kasar ya yi watsi da dokar sannan aka sake turawa kafin a sake yin watsi dashi a watan Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel