Boko Haram: AfDB ta ba Gwamnatin Najeriya Dala Miliyan 258

Boko Haram: AfDB ta ba Gwamnatin Najeriya Dala Miliyan 258

Mun ji labari Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa Babban bankin nan na cigaban Afrika watau AfDB zai narka kudi har Dala Miliyan 258 domin yin wasu ayyuka a cikin Yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Boko Haram: AfDB ta ba Gwamnatin Najeriya Dala Miliyan 258

Gwamnati za tayi wasu ayyuka a Arewa maso Gabas
Source: Facebook

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wannan jiya a babban Birnin Tarayya Abuja. Osinbajo ya bayyana wannan ne a wajen kaddamar da wannan shiri da aka tsara na IBSIP a Arewa maso Gabashin kasar.

Yemi Osinbajo yake cewa AfdB zai bada wannan kudi ne domin a gina abubuwan more rayuwa tare da kuma gyara Yankunan da Boko Haram su kayi ta’adi. Za kuma a ware kaso na wannan kudin wajen inganta rayuwar jama’a.

Mataimakin Shugaban kasar yana sa rai cewa za ayi aiki da wannan kudi wajen maida mutane fiye da Miliyan 2 da Boko Haram da su ka fatattaka zuwa gidajen su. Rikicin na Boko Haram ya rutsa da akalla mutane miliyan 1.4 a Yankin.

KU KARANTA: ‘Yan iskan Gari sun hana a rabawa ‘Yan kasuwa kudi a Ilorin

Farfesa Osinabjo yace Gwamnatin Buhari za ta cigaba da maida hankali wajen harkar kasuwanci da sana’o’i da kuma inganta ilmi da gyara muhalli da kuma samar da tsabtattaccen abinci da kuma habaka kiwon lafiya da wadannan kudi.

Bugu-da-kari, za a kashe kaso mafi tsoka na wannan kudi ne a kan Matasa da kuma Kananan yara inji Mataimakin Shugaban kasar. Hakan ne zai taimaka wajen kawo karshen rikicin Boko Haram wanda ya dabaibaye wasu Jihohin Kasar.

Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullah Abubakar da kuma Shugaban bankin AFDB wanda Ebrima Faal ya wakilta, su na cikin wadanda su ka halarci taron kaddamar da wannan muhimmin shiri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel