An haramtawa Inyamurai Mazauna Arewa komawa Mahaifarsu yayin Zaben 2019

An haramtawa Inyamurai Mazauna Arewa komawa Mahaifarsu yayin Zaben 2019

- Kungiyar kabilar Ibo ta IDA, Igbo Delegates Assembly, ta haramtawa al'ummar ta mazauna Arewacin Najeriya komawa mahaifar su a yayin zabe na 2019.

- Kungiyar za kuma ta ci tarar duk wanda ya sabawa wannan doka

-Kungiyar ta yanke wannan shawara yayin zaman da ta gudanar a unguwar Barnawa ta jihar Kaduna

Da sanadin shafin jaridar The Guardian, mun samu rahoton cewa, an haramtawa al'ummar kabilar Ibo mazauna jihohi 19 na yankunan Arewa komawa mahaifarsu domin kada kuri'un su a yayin babban zabe da za a gudabar a badi.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, duk wanda ya yiwa wannan sabuwar doka kunnen uwar shegu, za ya fuskanci hukunci na cin tara da kawowa yanzu ba a kayyade adadin ta ba.

An haramtawa Inyamurai Mazauna Arewa komawa Mahaifarsu yayin Zaben 2019

An haramtawa Inyamurai Mazauna Arewa komawa Mahaifarsu yayin Zaben 2019
Source: UGC

Kaddamar da wannan shawara gami da sabuwar doka ta biyo bayan wani zaman tattaunawa na musamman da kungiyar kabilar Ibo mazauna Arewa ta gudanar a unguwar Barnawa ta jihar Kaduna.

Kungiyar mai sunan Igbo Delegates Assembly, IDA, ta na jagorantar al'ummar kabilar Ibo mazauna jihohi 19 da ke Arewacin Najeriya da kuma garin Abuja, domin sauke nauyin da rataya a wuyan ta na tabbatar da jin dadin al'ummar ta.

KARANTA KUMA: Najeriya ta fi samun ci gaba a karkashin jagorancin PDP - Atiku

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an gudanar da taron na zartar da wannan sabuwar doka a tsakanin jagororin al'ummar Ibo da ke zazzaune cikin jihohi 19 na Arewacin Najeriya.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce tabbas shugaban kasa Muhammadu Buhari za ya sha babban kayi a hannunsa yayin zaben kasa na 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel