Yanzu-yanzu: Majalisar zantarwa ta tabbatar da kasafin kudin 2019, za'a gabatarwa yan majalisa

Yanzu-yanzu: Majalisar zantarwa ta tabbatar da kasafin kudin 2019, za'a gabatarwa yan majalisa

- Majalisar zantarwan tarayya FEC ta tabbatar da kasafin kudin 2019

- An tabbatar ne a taron FEC na musamman a yau Juma'a

Majalisar zantarwan tarayya ta tabbatar da shieyayyen kasafin kudin shekarar 2019 a ranan Juma'a, 7 ga watan Disamba, 2018. Mambobin majalisar sun tabbatar ne a zaman da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta daga karfe 10:30 na safe zuwa 1:30 na rana a fadar shugaban kasa.

Ministan kasafin kudi, Udoma Udoma ya sanar da hakan ne yayinda yake magana da manema labaran fadar shugaban kasa bayan taron FEC.

Yanzu-yanzu: Majalisar zantarwa ta tabbatar da kasafin kudin 2019, za'a gabatarwa yan majalisa

Yanzu-yanzu: Majalisar zantarwa ta tabbatar da kasafin kudin 2019, za'a gabatarwa yan majalisa
Source: Facebook

KU KARANTA: Masu juna biyu 30 ke mutuwa a Zamfara kulli yaumin - Kungiyar Likitoci

Udoma ya ce majalisar zata hada kai da majalisar dokokin tarayya domin sanin ranan da shugaba Buhari zai gabatar da takardan gabansu.

Yayinda aka bukaci bayani kan abubuwan dake cikin takardan, ya ce shugaban kasa kadai kundin tsarin mulki ta baiwa daman bayyana abinda ke ciki.

Yanzu-yanzu: Majalisar zantarwa ta tabbatar da kasafin kudin 2019, za'a gabatarwa yan majalisa

Yanzu-yanzu: Majalisar zantarwa ta tabbatar da kasafin kudin 2019, za'a gabatarwa yan majalisa
Source: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa wata zaman majalisan zantarwan tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta kankama a fadar shugaban kasa, Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja a ranan Juma'a, 7 ga watan Disamba, 2018.

Ana wannan zama ne domin tattaunawan karshe kan kasafin kudin 2019 kafin gabatar da shi gaban majalisar dokokin tarayya.

Yanzu-yanzu: Majalisar zantarwa ta tabbatar da kasafin kudin 2019, za'a gabatarwa yan majalisa

Yanzu-yanzu: Majalisar zantarwa ta tabbatar da kasafin kudin 2019, za'a gabatarwa yan majalisa
Source: Facebook

Gwamnatin tarayya tana son gabatar da kasafin kudin N8.6 Trillion sabanin N9.12tn da ta yi na shekarar 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel