Zaben 2019: Mun gama shiri tsaf - Hukumar 'yan sanda

Zaben 2019: Mun gama shiri tsaf - Hukumar 'yan sanda

- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce ta gama shiri domin tunkarar babban zaben 2019

- Hukumar ta kuma dauki alkawarin tabbatar da cewa an gudanar da sahihiyar zabe da al'umma za suyi na'am da shi

- Hukumar 'yan sandan ta ce ta tanadar da matakai na musamman da za su tabbatar da tsaro yayin zabe da bayan zaben

A jiya, Alhamis ne mataimakin Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mr Agboola Oshodi-Glover ya ce jami'an rundunar 'yan sandan sun kammala shirye-shirye domin tunkarar babban zaben 2019 da ke tafe.

Ya ce za su tabbatar an gudanar da sahihiyar zabe da al'umma za su yi na'am da shi kuma cikin lafiya.

Oshodi-Glover ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun a garin babban birnin jihar, Abeokuta.

Zaben 2019: Mun gama shiri tsaf - Rundunar 'Yan sanda

Zaben 2019: Mun gama shiri tsaf - Rundunar 'Yan sanda
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ba wan, ba kanin: Jam'iyyar AA taki amincewa da surukin Rochas

Shugaban 'yan sandan ya ce hukumar ta dauke matakai na musamman domin ganin an gudanar da sahihiyar zabe a shekarar ta 2019.

Ya ce, "Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gama shiri tsaf domin tunkarar zaben da ke tafe. Za mu tabbatar cewa mun samar da ingantaccen tsaro kafin zaben, lokacin da ake gudanar da zaben da kuma bayan kammala zaben.

"Rundunar yan sanda za ta tabbatar an gudanar da sahihiyar zabe mai inganci."

Shugaban 'yan sandan da ke ran gadin jihohin Kudu maso yamma domin wayar da kan 'yan sanda a kan ayyukan da za su gudanar lokacin zaben ya mika godiyarsa ga gwamnan saboda tallafin da ya bawa rundunar yayin da suke gudnaar da ayyukansu a jihar.

A lokacin da ya ke jawabinsa, Amosun ya jinjinawa hukumomin tsaron bisa yadda suka tabbatar da zaman lafiya da kiyaye dukiyoyin al'umma a sassa daban na kasar.

Ya shawarce su da su cigaba da gudanar nuna kwarewa yayin gudanar da ayyukansu yayin gudanar da zaben da ma bayan zaben.

Gwamnan kuma ya yabawa gwamnatin tarayya bisa yakin da takeyi da ta'addanci a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel