Rundunar Yansandan Najeriya ta bankado shirin kai hare hare da wasu miyagu ke yi a Benuwe

Rundunar Yansandan Najeriya ta bankado shirin kai hare hare da wasu miyagu ke yi a Benuwe

Rundunar Yansandan jahar Benuwe ta bayyana cewa ta bankado kulle kullen da wasu miyagun mutane ke yi na kai hari ga wani babban banki dake jahar kafin ranar bikin kirismeti, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Ene Okon ne ya sanar da haka a ranar Alhamis 6 ga watan Disamba yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin yansandan jahar dake, Makurdi.

KU KARANTA: Hukumar NDLEA ta yi nasarar kama miyagun kwayoyi da suka kai kilo 9, 607.72 a Kano

Kwamishina Okon yace a sakamakon bankado wannan shiri na miyagun mutane, rundunar Yansandan ta tsaurara matakan tsaro a dukkanin bankunan dake fadin jahar Benuwe don shirin ko ta kwana, kamar yadda suka karfafa tsaro a duk fadin jahar don gudanar da bikin kirismeti cikin kwanciyar hankali.

“Mun samu labarin cewa wasu miyagun matasa na kwararowa jahar Benuwe daga yankin kasar Inyamurai da nufin kai hari ga wani babban banki a jahar nan, don haka rundunar Yansanda ta tsaurara matakan tsaro a dukkanin bankunan dake jahar Benuwe.” Inji shi.

Bugu da kari kwamishina Okon ya bayyana cewa an kafa rundunar tsaro ta hadakan rundunonin Yansanda, Sojan ruwa, DSS, Sojan sama, Sojan kasa da na civil defence domin su zazzagaya lunguna da sakon jahar tare da sintirin manyan hanyoyin jahar.

A wani labarin kuma wasu gungun yan bindiga sun kai ma wata makarantar gaba da sakandari, kwalejin kimiyya ta jahar Osun dake garin Esa-Oke, farmaki a ranar Talata 4 ga watan Disamba inda suka sace malamai biyar tare da kashe wani jami’in kwalejin.

Sunan ma’aikacin kwalejin da yan bindigan suka kashe Olaniyi Temitope, inda rahotanni suka tabbatar da cewar yan bindigan sun kashe shine a wani harin mai kan uwa da wabi da suka yi a makarantar. daga bisani kuma yan bindigan suka yi awon gaba da malaman guda biyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel