Kotu ta yi umurnin kama jigon APC a Rivers kan zargin yunkurin aikata kisan kai

Kotu ta yi umurnin kama jigon APC a Rivers kan zargin yunkurin aikata kisan kai

Wata babbar kotu da ke Port Harcourt, jihar Rivers, ta yi umurnin kama Drakta Janar na kungiyar kamfen din Tonye Cole, Chidi Lloyd, kan zargin yunkurin kisan kai.

Alkalin kotun, Justis Chinwendu Nwogu, wanda ya bayar da umurnin kamun, ya bukaci kwamishinan yan sandan jihar da yayi gaggawan kama Lloyd, tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar.

Kotu ta yi umurnin kama jigon APC a Rivers kan zargin yunkurin aikata kisan kai

Kotu ta yi umurnin kama jigon APC a Rivers kan zargin yunkurin aikata kisan kai
Source: Facebook

Nwogu ya bayar da umurnin ne bayan rashin hallaran Lloyd da lauyansa a kotu lokacin fara sauraron shari’an yunkurin sa na aikata kisa a jiya.

Ana sanya ran tsohon dan majalisan zai gurfana akan shari’an da gwamnatin jihar ke yi a kansa mai lamba PH/692CR/2018 da PH/693 CR/2018.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsoro a Delta yayinda aka gano bam a kusa da gadar River Niger (hoto)

Alkalin yayi umurnin a tsare Lloyd a kurkukun tarayya na Port Harcourt zuwa ranar da za’a sake zama, ranar 10 ga wata Janairun 2019, sannan yan sanda su gurfanar dashi a kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel