An ci zarafin mata fiye da 500 a wata 10 a Kano - Inji wata Lauya

An ci zarafin mata fiye da 500 a wata 10 a Kano - Inji wata Lauya

Wata lauya a jihar Kano, Barista Maryam Ahmed Sabo, ta yi tsokaci akan matsalar cin zarafin mata da kananan yara musamman a Najeriya inda ta bayyana cewa lamarin na da girman gaske, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Barista Maryam ta ce an kiyasta cewa a cikin mata 10 a kan samu uku da aka ci zarafinsu ta hanyoyi daban-daban.

A cewarta ko a wajen tafiya da ake yi da mata fatauci ko safararsu, a kan matsa ma wasun su, ko a yi musu fyade ko kuma a tozartasu.

An ci zarafin mata fiye da 500 a wata 10 a Kano - Inji wata Lauya

An ci zarafin mata fiye da 500 a wata 10 a Kano - Inji wata Lauya
Source: UGC

Lauyar ta ce, baya ga cin zarafi ta hanyar fyade, a kan ci zarafinsu ta hanyar yi musu kaciya ko kuma fadan cikin gida.

Ta kara da cewa cin zarafin mata da kananan yara yafi yawaita a jihohin Lagas, Kano da kuma Borno, amma kuma duk da haka ba bu jihar da a Najeriya ba a samun wannan matsala ta cin zarafin mata.

Barista Maryam ta ce: "A jihar Kano kadai, tsakanin farkon shekara 2018 zuwa watan Oktoban shekarar, an ci zarafin yara fiye da 500."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsoro a Delta yayinda aka gano bam a kusa da gadar River Niger (hoto)

Ta bayyana sakacin iyaye da masu bayar da tarbiya a matsayin abunda ke haddasa faruwar haka. Haka kuma ta alakanta lamarin da rashin tsoron Allah na masu aikata hakan don kawai son biyan bukatar zuciyarsu.

Daga karshe ta alakanta lamarin ga daura wa yara mata talla, ko kuma yi masu auren dole wanda ke sa a ci zarafinsu ta hanyar duka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel