Yanzu Yanzu: Tsoro a Delta yayinda aka gano bam a kusa da gadar River Niger (hoto)

Yanzu Yanzu: Tsoro a Delta yayinda aka gano bam a kusa da gadar River Niger (hoto)

An samu tashin hankali da tsoro a tsakanin mazauna yanki Asaba karshen gadar Niger Delta biyo baya gano wani abu da ake zargin kayan fashea ne wato bam, jaridar Sun ta ruwaito.

Wasu ma’aikata da ke aiki gini ne suka gano abun yayinda suke hako kasa domin dasa tushen ginin shinge na rukunin C na rundunar yan sandan jihar Delta.

Ganin abun ya sanya ma’aikatan da mazauna yankin cikin rudani, yayinda wasu suka tsere domin tsira saboda gudun abunda ka iya zuwa ya komo.

Yanzu Yanzu: Tsoro a Delta yayinda aka gano bam a kusa da gadar River Niger

Yanzu Yanzu: Tsoro a Delta yayinda aka gano bam a kusa da gadar River Niger
Source: UGC

Shugaban yan sanda yankin, CSP Anietie Eyoh ya ki yayi Magana kana bun a lokacin da aka tunkare shi, amma ya bayyana cewa abunda ya fi muhimmanci gare shi shine lafiyar ma’aikatansa, ma’aikatan wajen da kuma yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnonin 9 masu mulki, da sabbin yan takara 20 ne za su yi takarar gwamna a APC - Oshiomhole

Da yake tabbatar da ganin bam din, kwamishinan yan sandan, Mista Anthony Ogbizi ya bayyana cewa jami’an sashin bam na rundunar sun dauke abun domin nazari akan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel