Ministar kudi, DMO da CBN sun yi wani zama da masu harkar man fetur a Najeriya

Ministar kudi, DMO da CBN sun yi wani zama da masu harkar man fetur a Najeriya

Mun ji labari cewa Ministar kudi ta Najeriya, Hajiya Zainab Ahmed ta gana da manyan ‘Yan kasuwan da ke harkar man fetur a Kasar domin domin ganin ba a samu wahalar mai a karshen shekarar nan ba.

Ministar kudi, DMO da CBN sun yi wani zama da masu harkar man fetur a Najeriya

Minista Zainab Ahmed ta zauna da masu kasuwancin man fetur
Source: Depositphotos

A jiya Alhamis 6 ga Wata ne aka yi wani zama na musamman a babban Birnin Tarayya Abuja da Ma’aikatar kudi na kasar da kuma babban Bankin Najeriya na CBN da kuma ofishin DMO mai kula da bashin da ke wuyan Najeriya.

Manyan Jami’an na Gwamnatin Tarayya sun gana da masu harkar man fetur a Kasar ne domin ganin ba ayi fama da wahalar mai a karshen shekara ba. Kungiyar IPMAN da sauran masu harkar fetur sun yi alkawarin ganin mai ya samu.

KU KARANTA: Majalisar Tarayya ta sa baki game da wahalar fetur na karshen shekara

Sakataren din-din-din na Ma’aikatar kudi ne ya wakilci Ministar a taron. A karshen zaman, an tabbatar da cewa masu hada-hadar fetur za su yi ta jigilar mai a tashoshin kasar babu kakkautawa a daidai lokacin da ake shirin bukukuwa.

Ma’aikatar kudin ta kuma bayyana cewa za a cigaba da tattaunawa bini-bini tsakanin Gwamnatin Tarayya da ‘Yan kasuwa domin shawo kan matsalolin da ke a tsakani. Kafin nan dai ‘Yan kasuwan sun yi barazanar zuwa yajin aiki a Kasar.

Kamfanin main a kasa watau NNPC ya shiga yarjejeniya da Kasar Turai inda za a cigaba da shigo da fetur Najeriya ba tare da yankewa ba a sa’ilin bukukuwan Kirismeti da kuma sabuwar shekara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel