Yan takarar kujeran Gwamna na APC 4 daga kudu maso gabas sun ziyarci Aso Rock

Yan takarar kujeran Gwamna na APC 4 daga kudu maso gabas sun ziyarci Aso Rock

- Yan takarar kujeran gwamna a jam’iyyar APC daga kudu maso gabas sun ziyarci fadar shugaban kasa

- Sun yi ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo

- Sai dai basu bayyana abunda ganawar ya kunsa ba

Yan takarar kujeran gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihohin kudu maso gabas sun ziyarci fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, 6 ga watan Disamba.

Yan takarar sun yi ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sannan sun ki bayyana dalilin ziyarar nasu, inda suka nace kan cewa lallai abune da ya shafi sirri.

Yan takarar kujeran Gwamna na APC 4 daga kudu maso gabas sun ziyarci Aso Rock

Yan takarar kujeran Gwamna na APC 4 daga kudu maso gabas sun ziyarci Aso Rock
Source: Facebook

Yan takarar hudu da suka kai ziyarar sune Sanata Ayogu Eze (Enugu); Hope Uzodinma (Imo); Sunny Uboji (Ebonyi) da kuma Uche Ogah (Abia).

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya shiga dimuwa – Tambuwal ya yi ba’a ga gwamnan Kaduna

A wani lamari na daban, mun ji cewa tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayyar Najeriya, Rt. Hon. Ghali Umar Na’abba ya tattara kayan sa ya bar Jam’iyyar APC mai mulki kamar yadda mu ka samu labari. Na’abba ya soki tsarin Jam’iyyar da ke mulkin Najeriya.

Kamar yadda labari ya iso mana, tsohon Shugaban Majalisar Kasar ya aikawa Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin sa da ke cikin Unguwar Sharada a cikin Birnin Garin Kano takarda inda ya bayyana ficewar sa daga Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel