Legas ta fi kowace Jiha a Najeriya samun kudin shiga a 2018 – NBS

Legas ta fi kowace Jiha a Najeriya samun kudin shiga a 2018 – NBS

Mun samu labari daga Jaridar Vanguard cewa wasu Jihohi za su gamu da cikas wajen samun kudi daga hannun Gwamnatin Tarayya a dalilin makudan bashi da su ka yi yawa a kan su, alhali kuma ba su da wani kudin shiga domin biyan bashin.

Legas ta fi kowace Jiha a Najeriya samun kudin shiga a 2018 – NBS

Za a rike kudin Jihohin da biyan bashi ke nema ya gagare su
Source: Depositphotos

Jihohin da yawan adadin bashin da ke kan su ke nema yayi kan-kan-kan da kudin shigar su, za su fuskanci babbar matsala, hakan na zuwa ne bayan Hukumar NBS mai tara alkaluma na kasa ta fitar da adadin abin da kowace Jiha ta ke samu.

Rahotannin da Hukumar ta NBS ta fitar na kason farkon shekarar nan ta 2018 ya tabbatar da cewa bashi yayi wa wasu Jihohi yawa. Haka kuma dai abin da Jihohin ke samu ta hanyar kudin shiga ya karu daga Naira Biliyan 450 zuwa Biliyan 579.

KU KARANTA: APC ta bayyana wadanda za su rike mata tuta a zaben Gwamnoni

Jihohi 28 ne su ka kara himma wajen tatsar kudin shiga yayin da wasu Jihohi 8 kuma su ka ci baya. Daga cikin Jihohin da lamarin su ya kara tabarbarewa kamar yadda mu ka ji akwai irin su Ebonyi, Anambra, Benuwai, Abia da kuma Jihar Kebbi.

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa har gobe dai Legas ce kan gaba wajen samun kudin shiga a kaf Najeriya. A cikin ‘yan watannin shekarar nan, Legas ta samu kusan Naira Biliyan 400. Jihar Ribas ce mai Naira Biliyan 60 ke takewa Legas baya.

A karshe dai rahoton da NBS ta fitar ya nuna cewa kudin da Jihohi su ke samu daga asusun Tarayya ya karu matuka a bana. A cikin watanni 6, Jihohi 36 sun raba fiye da Naira Tiriliyan 1.2, a daidai wannan lokaci a bara kuwa Biliyan 700 aka samu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel