An ki bari a ba ‘Yan kasuwa gudumuwar TraderMoni a Jihar Kwara

An ki bari a ba ‘Yan kasuwa gudumuwar TraderMoni a Jihar Kwara

- Tsageru sun hana Jami’an Gwamnati raba tallafin Trader Moni

- Wadannan Matasa sun hana a bada gudumuwa a kasuwar Ilorin

- Jama’a sun ci buri za su samu wannan kudi amma aka tada rikici

An ki bari a ba ‘Yan kasuwa gudumuwar TraderMoni a Jihar Kwara

Rikici ya sa an gaza rabawa 'Yan kasuwa kudin TraderMoni a kasuwar Ilorin
Source: Twitter

Mun samu labari daga Hukumar NAN mai dillacin labarai a Najeriya cewa wasu tsageru sun kawo hatsaniya a cikin Garin Ilorin a Jihar Kwara a daidai lokacin da Jami’an Gwamnati ke shirin raba tallafin nan na TraderMoni jiya da safe.

Wadannan fitinannun mutane sun hargitsa kasuwar Garin Ilorin a sa’ilin da ake kokarin bada gudumuwa ga masu karamin karfi a cikin kasuwar. Kamar yadda mu ka samu labari, wadannan Matasa su na sanye ne rigunan Atiku.

KU KARANTA: APC ba ta san abin da take yi ba inji tsohon Shugaban Majalisa

An ce wadannan Matasa sun iso kasuwar ne dauke da hotunan ‘Dan takarar PDP na Shugaban kasa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP inda su ka hana Ma’aikatan Gwamnati raba kudin da aka soma badawa ga kananan ‘yan kasuwa.

Wadannan Bayin Allah sun bada korafin cewa Mahaifin Shugaban Majalisar Dattawa, Olusola Saraki, shi ne wanda ya bada filin da aka gina wannan kasuwa a Garin don haka Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ba za su yi wannan aiki a kasuwar ba.

Jami’an BOI na Gwamnatin Tarayya sun yi kokarin bada N10, 000 ne ga masu kananan kasuwanci a cikin Jihar Kwara kamar yadda aka soma tuni, amma abin ya gagara. Hakan ta sa dai dole aka kira Jami’an tsaro domin gudun wata fitina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel