APC ta bangare a Jihar Imo yayin da wasu su ke komawa Jam’iyyar AA

APC ta bangare a Jihar Imo yayin da wasu su ke komawa Jam’iyyar AA

- Gwamna Rochas Okorocha ya rantse sai Surukin sa yayi Gwamna a Imo

- Wannan ya sa Nwosu ya koma Jam’iyyar AA bayan ya rasa tikitin APC

- Yanzu ‘Yan Jam’iyyar APC sun rabu 2 tsakanin Jam’iyyar da kuma AA

APC ta bangare a Jihar Imo yayin da wasu su ke komawa Jam’iyyar AA

Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha a wajen taron APC
Source: Depositphotos

Jaridar Vanguard ta rahoto labari inda tace da alamu, Gwamna Rochas Okorocha ya gamu da cikas a Jam’iyyar APC na Jihar Imo a wajen kokarin da yake yi na tsaida Surukin sa takara a Jam’iyyar hamayya ta Action Alliance.

Wasu daga cikin manyan Jam’iyyar APC a Jihar Imo sun tuburewa Gwamna Rochas Okorocha inda su ka ki bin Mista Uche Nwosu zuwa Jam’iyyar AA kamar yadda Gwamnan ya nema. Kwanaki ne ‘Dan takarar ya bar APC ya koma AA.

Gwamna Okorocha ne dai yake kokarin kakaba Uche Nwosu a matsayin Magajin sa a 2019 ko ta halin ka-ka inda har ta kai Surukin na sa ya sauya-sheka zuwa Jam’iyyar AA, bayan ya rasa tikitin APC a hannun Sanata Uzodinma.

KU KATANTA: Rochas Okorocha ya nemi Buhari ya ja kunnen Shugaban Jam'iyyar APC

Yanzu dai wasu Jagororin APC su na tare da Hope Uzodinma inda su ka ki sauya-sheka tare da wanda Gwamna Okorocha ya tsaida takara. Uzodinma da wasu kusoshin APC a Jihar, sun nemi NWC ta rusa shugabannin ta na Imo.

Sakataren yada labarai na APC a Imo, Onwuasoanya Jones yana cikin wadanda su ka koma Jam’iyyar AA kwanaki, ana kuma tunani kwanan nan wasu daga cikin wadanda ake ji da su za su iya bin ‘Dan takarar Gwamnan zuwa AA.

Wata kungiya da ta bayyana daga cikin Jam’iyyar APC mai suna Rescue Mission tana tare da Uwar Jam’iyya inda tayi baram-baram ga Gwamna Okorocha. Wasu na-hannun daman Gwamnan kuwa su na ganin AA za ta kai labari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel