Najeriya ta fi samun ci gaba a karkashin jagorancin PDP - Atiku

Najeriya ta fi samun ci gaba a karkashin jagorancin PDP - Atiku

- Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin PDP ta yiwa ta APC fintinkau ta fuskar tabbatar da ci gaba da nasarar kasar Najeriya

- Turakin Adamawa ya sha alwashin sauya fasalin Najeriya bayan watanni shidda da karbar jagorancin kasar nan

- Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP ya kirayi 'yan Najeriya kan tumbuke shugaba Buhari daga kujerar mulki yayin babban zabe na 2019

A jiya Alhamis, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayin kamanta gwamnatocin PDP da suka shude da kuma gwamnatin jam'iyyar APC mai ci a yanzu, ya fedewa jam'iyyar ta APC Biri har wutsiya da cewar PDP ta yi fintinkau ta kowace siga ta samar ci gaba.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a harabar taro ta Mapo da ke birnin Ibadan na jihar Oyo, yayin gudanar da yakinsa na neman zaben kujerar shugaban a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Atiku ya sha alwashin sauya fasalin kasar nan tare da tabbatar da yi ma ta garambawul bayan watanni shidda da karbar ragamar mulkin kasar nan.

Najeriya ta fi samun ci gaba a karkashin jagorancin PDP - Atiku

Najeriya ta fi samun ci gaba a karkashin jagorancin PDP - Atiku
Source: Facebook

Turakin na Adamawa ya kuma yi babatu dangane da yadda gwamnatin jam'iyyar APC ta haddasawa kasar nan afkawa cikin kangi da katutu na tsananin bashi, inda ya ce dole 'yan Najeriya su mike tsaye wurjajan wajen fatattakar shugaban kasa Buhari daga kujerar sa a zaben 2019.

Jiga-jigan da ke cikin tawagar Atiku yayin wannan taro sun hadar da; abokin takararsa, Peter Obi; shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus; shugaban kungiyar yakin neman zabensa, Otunba Gbenga Daniel; tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose da kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Prince Olagunsoye Oyinlola.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya ba su da hujjar sake zaben Buhari - Sanata Olujimi

Tawagar ta Atiku kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito ta bayyana takaicinta dangane da yadda Talauci, Yunwa da kuma rashin tsaro suka zamto tamkar karfen kafa ga al'ummar kasar nan.

Kazalika shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya halarci wannan taro inda ya yi kira ga al'ummar kasar na kan kawo karshen kalubalen da suke fuskanta ta hanyar tumbuke gwamnatin jam'iyyar APC a yayin babban zabe na badi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel