An bada belin Deji Adeyanju bayan tsawon kwanaki a daure

An bada belin Deji Adeyanju bayan tsawon kwanaki a daure

Mun samu labari cewa wata babbar Kotun Majisatare da ke Unguwar Wuse II a cikin babban Birnin Tarayya Abuja ta bada izini a saki Deji Adeyanju wanda aka kama aka garkame kwanan nan.

An bada belin Deji Adeyanju bayan tsawon kwanaki a daure

Kotu ta saki Deji Adeyanju daga gidan kurkukun Keffi
Source: UGC

Kotun ta bada belin Deji Adeyanju ne a kan kudi N500, 000 tare da kawo wasu manyan Ma’aikatan Gwamnati 2 da za su tsaya masa. Alkali mai shari’a Idayat Akanni ta Kotun ce ta yanke hukuncin cewa a bada belin wannan Matashi.

Kamar yadda labari ya zo mana daga wata Jaridar Kasar nan, ba a bata lokaci ko kadan ba, wajen cika sharudan belin da Kotu ta gindayawa wannan Bawan Allah. An dai garkame Adeyanju ne a gidan kurkukun da ke Garin Keffi.

Shugaban Hafsun Sojin kasa, Janar Tukur Yusuf Buratai ne yam aka karar wannan mai fafatukar karbo hakkin Jama’a a Kasar. Janar T.Y Buratai yana zargin Mista Adeyanju da agazawa ‘Yan ta’adda a kafofin sa na sadarwa na zamani.

KU KATANTA: Sakamakon Zaben 2019 zai haskaka kudirin al'ummar Najeriya - Buhari

A baya dai mun ji cewa ana zargin Adeyanju Deji wanda shi ne Shugaban kungiyar nan ta 'Concerned Nigerians' da kokarin batawa Jami'an Sojoji da kuma ‘Yan Sanda suna da kuma addabar al’umma tare da yi wa Jami’an tsaro kutse .

Sai dai yanzu Jami’an tsaron da su ka damke Adayanju sun yi watsi da wasu daga zargin bayan sun shigar da kara a gaban Kotu. Ko da dai masu karar ba su bayyan yadda Deji Adeyanju ya batawa Sojojin kasar Najeriyar suna ba.

Lokacin da abin ya faru Kungiyar nan ta Amnesty International ta reshen Najeriya ta bayyana cewa daure Mista Adeyanju Deji da sauran takwarorin da aka yi, yana cikin keta hakkin Bil–Adama da kokarin hana Jama’a ta-cewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel