APC ba ta da alkibla don haka na fice na bar ta – Inji Ghali Na’Abba

APC ba ta da alkibla don haka na fice na bar ta – Inji Ghali Na’Abba

- Ghali Na’Abba yace Jam’iyyar APC sam ba ta san abin da ta ke yi ba

- Rt. Hon. Na’Abba ya soki tsare-tsaren Jam’iyyar da ke mulkin kasar

- Tsohon Shugaban Majalisar yace Gwamnoni sun yi kememe a APC

APC ba ta da alkibla don haka na fice na bar ta – Inji Ghali Na’Abba

Rt. Hon. Ghali Na’Abba ya fice daga APC, yayi kaca-kaca da Jam'iyya
Source: Facebook

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayyar Najeriya, Rt. Hon. Ghali Umar Na’abba ya tattara kayan sa ya bar Jam’iyyar APC mai mulki kamar yadda mu ka samu labari. Na’abba ya soki tsarin Jam’iyyar da ke mulkin Najeriya.

Kamar yadda labari ya iso mana, tsohon Shugaban Majalisar Kasar ya aikawa Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin sa da ke cikin Unguwar Sharada a cikin Birnin Garin Kano takarda inda ya bayyana ficewar sa daga Jam’iyyar.

Ghali Na’Abba ya tsere daga APC ne a tsakiyar makon nan inda ya bayyana yadda Jam’iyyar ta ke juya Kasar a matsayin dalilin sa na canza-sheka. Na’Abba yace kowa ya san irin halin da Jam’iyyar ta jefa al’ummar Najeriya.

KU KARANTA: Wani Gwamnan APC ya nemi Buhari ya ja kunnen Adams Oshiomhole

Hon. Na'Abba yayi Allah-wadai da yadda APC tayi sanadiyyar rigingimu iri-iri a kusan kowane Jiha na fadin kasar nan. Haka kuma yace rashin iya mulkin APC ya sa Jam’iyyar ta rasa shugabancin Majalisun Kasar nan a hannun PDP.

Tsohon ‘Dan Majalisar yace Gwamnonin APC sun handame komai a Jam’iyyar, sannan kuma an hana Jama’a su ce uffan. Na’Abba yace wadannan abubuwa dai sun kawowa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikas a mulkin sa.

Hon. Ghali Na’Abba yace ba zai cigaba da zama a wannan tsari da ake yaudarar jama’a da sunan yaki da barayi ba alhali jama’a su na cutuwa. Yanzu dai tsohon ‘Dan Majalisar Tarayyar Kasar bai bayyana mana Jam’iyyar da ya koma ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel