'Yan Najeriya ba su da hujjar sake zaben Buhari - Sanata Olujimi

'Yan Najeriya ba su da hujjar sake zaben Buhari - Sanata Olujimi

Shugaba maras rinjaye a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Biodun Olijimi, ta bayyana cewa 'yan Najeriya ba su da wata hujja ko da kuwa ta Sisin Kobo ce ta sake zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin babban zabe na 2019.

Olujimi, wadda ta kasance 'yar takarar kujerar Sanata shiyyar Ekiti ta Kudu a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, 'yan Najeriya su yi duba bisa ga tafarkin cancanta da kuma ikon tabbatar da jagoranci nagari yayin kada kuri'un su a zaben na badi.

Sanata Olujimi ta bayyana hakan ne da sanadin jagoran kungiyar yakin neman zaben ta, Sanya Adesua, cikin kauyen Ikere yayin rarraba littafai na darussan Lissafi da kuma Turanci ga Makarantun gwamnati da ke mazabarta a Kudancin jihar Ekiti.

Shugaba a majalisar ta dattawan ta kuma bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya gaza ta kowace siga akan karagar mulkin kasar nan da ba ya da ta cewa wajen kafa hujjojin sa yayin yakin neman zabe.

Buhari - Sanata Olujimi - Atiku

Buhari - Sanata Olujimi - Atiku
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sanata Olujimi ta yiwa shugaba Buhari wankin babban bargo da a cewar ta ba bu wani tasiri da jagorancin sa na tsawon shekaru hudu ya haifar a kasar nan.

Ta ci gaba da cewa, kasawar shugaba Buhari bisa kujerar mulki ta sanya ya gaza fuskantar al'ummar kasar domin baje ma su dalilai gami da hujjoji da za su sanya ya samu goyan baya yayin babban zabe na 2019.

KARANTA KUMA: Sakamakon Zaben 2019 zai haskaka kudirin al'ummar Najeriya - Buhari

Sanata Olujimi ta kuma kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta gaza wajen samar da tsaro matabbaci a kasar nan, baya ga yunwa gami da talauci da ya yiwa al'umma katutu kuma uwa uba zangwanyewar tattalin arziki.

A yayin haka kum Sanata Olujimi ta shawarci al'ummar kasar nan kan sanya amincinsu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, inda ta ce zabensa shi kadai ne tafarkin tsira a Najeriya da za ya fidda A'i daga Rogo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel