Gabanin zaben 2019: INEC ta nada sabon Sakatariya

Gabanin zaben 2019: INEC ta nada sabon Sakatariya

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta nada Rose Orianran-Anthony a matsayin sabuwar Sakatariyar hukumar

- Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Festus Okoye, kwamishina na kasa kuma shugaban kwamitin watsa labarai da ilimin zabe na hukumar

- A cewar sanarwar, ta kwashe shekaru 28 tana aiki a hukumar, inda ta rike mukamai da dama da suka hada da jami'ar hulda da jama'a, manajar kula da shafin INEC na yanar gizo

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta nada Rose Orianran-Anthony a matsayin sabuwar Sakatariyar hukumar.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Festus Okoye, kwamishina na kasa kuma shugaban kwamitin watsa labarai da ilimin zabe na hukumar, wanda ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

"Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, a taronta na karshen mako, ta amince da nadin Mrs. Rose Orianran-Anthony a matsayin Sakatariyar hukumar, bisa yarjejeniyar aiki na shekaru 4, wanda zai fara daga ranar 6 ga watan Disamba 2018," a cewar sanarwar.

KARANTA WANNAN: Rundunar sojin Najeriya na bukatar N9bn don siyan takalman sojoji a duk shekara

Gabanin zaben 2019: INEC ta nada sabon Sakatariya

Gabanin zaben 2019: INEC ta nada sabon Sakatariya
Source: Depositphotos

Mrs.Orianran-Anthony, yar asalin jihar Edo ce, wacxe ke da matakin karatu na Degree a ilimin sanin yaruka daga jami'ar Ahmadu Bello, tare da matakin karatu na Masters a ilimin sadarwar jama'a da hulda da jama'a daga jami'ar Westminster da ke Landan.Mrs.Orianran-Anthony, yar asalin jihar Edo ce, wacxe ke da matakin karatu na Degree a ilimin sanin yaruka daga jami'ar Ahmadu Bello, tare da matakin karatu na Masters a ilimin sadarwar jama'a da hulda da jama'a daga jami'ar Westminster da ke Landan.

A cewar sanarwar, ta kwashe shekaru 28 tana aiki a hukumar, inda ta rike mukamai da dama da suka hada da jami'ar hulda da jama'a, manajar kula da shafin INEC na yanar gizo, da kuma shugabar sashen kula da harkokin kungiyoyin fararen hula, gabaninnadata wannan matsayi, ta rike mukamin darakta, sai kuma Sakatariyar ayyuka a ofishin hukumar da ke jihar Delta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel