Buhari sai ya fadi, in ji Atiku

Buhari sai ya fadi, in ji Atiku

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya ce shugaba Buhari ya gama faduwa zaben shekarar 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya fadi haka ne a garin Ibadan, yayin kaddamar da yakin neman zabensa a yankin kudu maso yamma.

"Sai Buhari ya tafi! Sai Buhari ya tafi! Sai Buhari ya tafi!" Atiku ya fada tare da taron magoya bayansa.

DUBA WANNAN: Aikin gwamna na da wahala, ji nake tamkar na tsere - El-Rufa'i

Ya yi kira ga magoya bayansu suyi watsi da alkawurran da jam'iyyar APC da Buhari ke jagoranci za tayi mu su.

Buhari sai ya fadi, in ji Atiku

Buhari sai ya fadi, in ji Atiku
Source: Facebook

Ya ce ilimi mafi inganci da 'yan Najeriya suka samu, sun same shi ne lokacin da jam'iyyar PDP ke mulki.

"Bari in fada muku yau, cikin wattani shida da zaban mu, za mu fara aikin gyaran tsarin rabon arzikin Najeriya, inji Atiku Abubakar.

"Na zauna a jihar nan saboda haka ni ba bako bane saboda haka na ke fada muku kada ku sake amincewa da da APC.

"Nan da watanni biyu za ku zabi shugabanku, ina rokon ku da kuyi nazari kafin zaben shugaban.

"Demokuradiyya mafi kyau da Najeriya ta mora shine karkashin PDP. A shekarar 2015, APC tayi alkawarin samar da ayyukan yi miliyan 12 amma har yanzu ba mu ga ayyukan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel