Aisha ta nemi 'yan Najeriya su yaki mutane 2 da suka hana ruwa gudu a Najeriya, bidiyo

Aisha ta nemi 'yan Najeriya su yaki mutane 2 da suka hana ruwa gudu a Najeriya, bidiyo

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta kalubalanci 'yan Najeriya a kan su tashi tsaye domin yakar wasu mutane biyu da suka hana ruwa gudu a gwamnatin mijinta.

Uwargidan shugaban kasar na wadannan kalamai ne yayin halartar wani taron mata masu goyon bayan Buhari da Osinbajo su maimaita mulki

Duk da bata ambaci sunayen mutane biyu ba, ta bayyana cewar sun kankane komai a gwamnatin da mutum miliyan 15 suka zaba.

Aisha ta nemi 'yan Najeriya su yaki mutane 2 da suka hana ruwa gudu a Najeriya, bidiyo

Aisha ta nemi 'yan Najeriya su yaki mutane 2 da suka hana ruwa gudu a Najeriya, bidiyo
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan majalisar dokokin jihar Imo 18 sun fita daga jam'iyyar APC

"Ba zamu yarda da wannan tsari da wasu mutum biyu kacal zasu kankane komai a gwamnatin da mu miliyan 15.4 muka zaba ba a shekarar 2015.

"Idan har mutum biyu zuwa uku zasu mamaye komai a gwamnatin da fiye da mutum miliyan 15 suka kafa, sai mu tambayi ina mazan suke a Najeriya? Me kuke yi? maimakon ku fito ku yaki wadannan mutane, kun buge da ziyartar su duk inda suke kuna yi masu banbadanci (ku yi hakuri nayi amfani da wannan kalma)," a cewar Aisha.

Wannan ba shine karo na farko da Aisha ta fara nuna fushinta a kan wasu mutane dake tare da shugaba Buhari ba.

Ko a shekaru biyu da suka wuce haka tayi banbami a kan irin wadannan mutane yayin wata hira da kamfanin jaridar kasar Ingila (BBC).

Ku kalli faifan bidiyon abinda ta fada a wurin taron matan:

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel