Yanzu Yanzu: Anyi gagarumin sauyi a hukumar sojin Najeriya, sabbin jami’ai za su yi yaki da ta’addanci a arewa maso gabas

Yanzu Yanzu: Anyi gagarumin sauyi a hukumar sojin Najeriya, sabbin jami’ai za su yi yaki da ta’addanci a arewa maso gabas

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai a ranar Alhamis, 6 ga watan Disamba ya bayyana cewa wasu sabbin jami’ai da aka yiwa karin girma za su koma yankin arewa maso gabas domin karfafa yaki da ta’addanci da ke gudana.

Buratai ya bayar da tsokacin ne a ranar Alhamis, a Abuja bayan ya kawata sabbin Manjo Janar 29 da wasu Birgediya Janar da sabbin mukamansu.

Yanzu Yanzu: Anyi gagarumin sauyi a hukumar sojin Najeriya, sabbin jami’ai za su yi yaki da ta’addanci a arewa maso gabas

Yanzu Yanzu: Anyi gagarumin sauyi a hukumar sojin Najeriya, sabbin jami’ai za su yi yaki da ta’addanci a arewa maso gabas
Source: Depositphotos

“Wasu daga cikinku da aka yiwa Karin girma a yau; muna jiran yau ne kawai sannan zuwa gobe ina sanya ran cewa za ku kwashi jakunkunanku ku tafi yankin arewa maso gabas.

“Wasu daga cikinku baku da zabin da ya wuce tafiya chan kai tsaye.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ministan muhalli ya zama sarkin Nasarawa

“Takardan sauyin ya rigada ya fito,” inji shi sannan ya umurci sakataren rundunar da ya karanta ga jami’an da abun ya shafa.

Sannan Buratai ya ba matan wadanda abun ya shafa hakuri da su kula da gida da kyau yayinda mazajensu za su kasance achan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel