Zanga-zangan majalisar dokoki: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga ministar kudi

Zanga-zangan majalisar dokoki: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga ministar kudi

Majalisar wakilai a ranar Alhamis, 6 ga watan Disamba ta aika sammaci ga ministar kudi, Zainab Ahmed, kan zanga-zanga da ma’aikatan majalisar dokoki karkashin kungiyar Parliamentary Staff Association of the National Assembly (PASAN) suka yi.

A cewar sammacin, ministar kudin zata gurfana a gaban kwamitin kudi na majalisar dokokin don tayi bayanin dalilin da yasa ba’a saki kudaden majalisar dokoki da na bangaren shari’a ba kamar yadda yake a kasafin kudin 2018.

Shugaban kwamitin dokoki da kasuwanci na majalisar, Edward ya bayyana yadda zanga-zangan ma’aikata na ranar 4 ga watan Disamba ya kawo tsaiko ga ayyukan yan majalisa.

Zanga-zangan majalisar dokoki: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga ministar kudi

Zanga-zangan majalisar dokoki: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga ministar kudi
Source: Depositphotos

Ma’aikatan sun dai yi zanga-zanga ne akan rashin biyansu kudadensu da kuma rashin Karin girma ga wasun su da ya kamata ace anyi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Anyi gagarumin sauyi a hukumar sojin Najeriya, sabbin jami’ai za su yi yaki da ta’addanci a arewa maso gabas

Da yake jawabi ga manema labarai, mai Magana da yawun majalisar, Abdulrazak Namdas (APC, Adamawa) ya ce yan majalisar sun aika sammaci ga ministar kudi domin tayi bayanin dalilin da yasa ba’a saki kaso 28 na Karin albashin da ma’aikata suka nema ba duk da cewar yana cikin kasafin kudin 2018.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel