Matasan NOTtooYoungToRun sun yunkuro don sanya samari da 'yan mata a turba ta shiga gwamnati

Matasan NOTtooYoungToRun sun yunkuro don sanya samari da 'yan mata a turba ta shiga gwamnati

- Kafaffiyar kungiyar Matasa masu neman shiga a dama dasu a gwamnati, tace zata horas da 'yan takarar ta dan samun nasara a zabe mai zuwa

- Suna bukatar hakan saboda dayawa daga cikin su wannan shine karo na farko da suka shiga cikin harkar siyasa

- Wannan dama da matasa suka samu zai janyo canji akan harkar siyasa

Kamfanin giya ya kai agaji makarantun jihar shari'a ta Kano, sun kuwa amsa

Kamfanin giya ya kai agaji makarantun jihar shari'a ta Kano, sun kuwa amsa
Source: Depositphotos

A ranar Laraba kafaffiyar kungiyar nan ta "Not Too Young to Run Movement" zata horas da matasan da suka tsaya takara akan yanda zasu gudanar da harkar camfe na zaben shekara ta 2019.

Mamba ta kungiyar Yetunde Bakare ce ta bayyana manema labarai hakan a yayin da suke gudanar da wani taro.

Ms Bakare tace wannan tafiya suna yinta ne dan ganin sun kawo sauyi akan harkar siyasar kasar da kuma ganin an fitar da bara gurbi a harkar zabe.

Ta kara da cewa yana da matukar amfani a garesu dasuyi wannan horas wa duba da cewa da yawa daga cikin matasan wannan shine karansu na farko da suka tsunduma harkar siyasa.

Bayan doka ta bawa Wannan kungiya dama da yawa daga cikin 'ya'yan ta sun suna sha'awar su ta tsayawa takara wanda yawan su yakai mutane 400.

DUBA WANNAN: Nafi karfin maula a hannun 'yan siyasa - Oyedepo ke maida martani bayan katobaras Father Mbaka kan kin sadaqar Peter Obi ga Coci

Matasan yan siyasa daga jam'iyu 91 ne zasu amfana d wannan horas wa wadda za'a gudanar a Abuja.

Hamzat Lawan wani mamba a kungiyar yace tunda doka ta amincewa kungiya to fa yanayin siyasa zai canja salo.

Mr Lawan ya kara da cewa wannan taro wanda zai gudana a ranar 10 ga watan Disamba zai nusar da matasan abubuwa da dama sannan su guji bin iskar da zata rinjaye su su fadi a shugabanci dama a gwamnatance.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel