Kotu ta tsare tsohon gwamnan Kebbi da wasu 2 a hannun EFCC

Kotu ta tsare tsohon gwamnan Kebbi da wasu 2 a hannun EFCC

Wata babbar kotun tarayya da ke Birnin Kebbi, jihar Kebbi karkashin jagorancin Justis Basse Onu a ranar Alhamis, 6 ga watan Disamba ta tsare tsohon gwamnan jihar, Alhaji Saadu Usman Dakingari, tare da wani Sunday Dogoyaro da kuma Garba Kamba a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), a Birnin Kebbi zuwa ranar da za’a yanke hukunci akan belinsu a ranar 10 ga watan Disamba.

Wadanda ake karan na fuskantar tuhume-tuhume 13 daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa kan zargin zambar kudade.

Ana zarginsu da satar kudi naira miliyan 450, daga cikin dala miliyan 115 da dala miliyan 115 da aka karba daga tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke wanda ya saba ma sashi na 1A na dokar satar kudi na 2015 da sauransu.

Kotu ta tsare tsohon gwamnan Kebbi da wasu 2 a hannun EFCC

Kotu ta tsare tsohon gwamnan Kebbi da wasu 2 a hannun EFCC
Source: Twitter

Sai dai dukkanin wadanda ake karan sun ki amsa dukka tuhumar da ake yi masu yayinda lauyan mai kara ya bukaci kotu da ta fara shari’ansu ba da bata lokaci ba.

Don haka lauyoyin wadanda ake kara sun nemi kotu da ta ba wadanda suke karewa beli.

KU KARANTA KUMA: 2019: Bayan kayar da Buhari da zan yi harda ritaya zan yi masa – Atiku

Da yake martani ga bukatar lauyoyin wadanda ake kara, lauyan EFCC, J. A. Ojogbane wanda bai ja da bukatar nasu ba, ya roki kotu da cewa hukumar na da wajen tsare wadanda ake tuhuma a Birnin Kebbi da Sokoto ana iya tsare wadanda ake karan kafin ranar da aka dage.

Yayinda yake yanke hukunci kan belin, Justis Onu ya yi umurnin tsare wadanda ake karan su uku a wajen tsare mutane na hukumar da ke Birnin Kebbi zuwa lokacin da za’a bayar da belin nasu a ranar 10 ga watan Disamba sannan an dage sauraron karar zuwa wannan rana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel