Dalilin da yasa ba zan kara yin korafi da gwamnatin da na gada ba - Buhari

Dalilin da yasa ba zan kara yin korafi da gwamnatin da na gada ba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ba zai kara yin korafi da gwamnatocin baya na jam'iyyar PDP da suka haddasa matsalolin da yanzu gwamnatinsa ke fuskanta ba.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake bayyana takaicinsa dangane da matsalar cin hanci da rashawa ga 'yan Najeriya mazauna kasar Poland.

Mai taimaka shugaba Buhari a harkokin kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, ce ta shirya taron domin bawa 'yan Najeriya mazauna kasar Poland damar ganawa da jami'an gwamnatin Najeriya domin tattaunawa a kan al'amuran da suka shafi mulki.

Dalilin da yasa ba zan kara yin korafi da gwamnatin da na gada ba - Buhari

Buhari a kasar Poland
Source: Facebook

"Mun gaji matsaloli masu yawan gaske; sai dai na riga na yi alkawarin cewar zan daina korafi a kan hakan saboda ni na daukowa kaina aikin shugabancin Najeriya.

DUBA WANNAN: Ministan kwadago ya karbi ragamar tattaunawa da ASUU

"Sau uku ina takarar takarar neman zama shugaban kasar Najeriya kafin na samu a karo na hudu, saboda haka yin korafi ba nawa bane.

"Babu wanda ya tilasta min sai na zama shugaban kasa. Sau uku ina zuwa kotu a kan zabe. Amma a karo na hudu, da taimakon Allah da na fasahar na'urar tantancewa, sun kasa yin magudin da suka yi min, nayi nasara a kansu," a kalaman Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel