Gwamnan Jihar Imo Okorocha yayi tir da Oshiomhole saboda sukar Obasanjo

Gwamnan Jihar Imo Okorocha yayi tir da Oshiomhole saboda sukar Obasanjo

Mun ji labari cewa Gwamnan Jihar Imo watau Rochas Okorocha ya jawo hankalin Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole.

Gwamnan Jihar Imo Okorocha yayi tir da Oshiomhole saboda sukar Obasanjo

Gwamna Okorocha ya fadawa Buhari ya ja hankalin Shugaban APC
Source: Depositphotos

Gwamna Rochas Okorocha ya fitar da wani jawabi ne ta bakin babban Sakataren yada labaran sa, Sam Onwuemeodo inda ya nemi a fadawa Adams Oshiomhole ya bi a hankali game da yadda yake jan ragamar shugabancin Jam’iyya.

Rochas Okorocha yake cewa idan ba a manta ba, irin baram-baramar da Adams Oshiomhole yake yi na ta sa PDP ta sha kasa a zaben 2015. Gwamnan yace ko Buhari bai taba zagin kowa a kasar ba kamar yadda shi Oshiomhole yake yi.

KU KARANTA: Atiku da Obasanjo za su dauki kashin su a hannu a 2019 – Shugaban APC

Mai Girma Gwamnan ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda Shugaban na APC yake caccakar irin su Mai Girma tsohon Shugaban kasa Oluesegun Obasanjo. Gwamnan na Imo yace bai kamata a rika zagin manyan Dattawan kasa ba.

Kwanan nan ne aka ji Oshiomhole yana cewa Ubangiji zai yi maganin Oluesgun Obasanjo tare da kuma caccakar wasu Gwamnonin na APC. Gwamna Okorocha yace duk da banbancin siyasa, sam bai dace a rika taba irin su Obasanjo ba.

Dazu kun ji yadda Adams Oshiomhole ya dura kan ‘Dan takarar Shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da kuma tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo inda yace dukkan su za su sha kunya a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel