Ba za ayi fama da matsalar man fetur a Disamban bana ba – Majalisar Tarayya

Ba za ayi fama da matsalar man fetur a Disamban bana ba – Majalisar Tarayya

- Majalisar Tarayya tana sa rai ba za ayi wahalar man fetur a karshen shekarar nan ba

- Kwamitin harkokin man fetur a Majalisa ta bada wannan tabbaci a cikin makon nan

- Kamfanin NNPC yayi tanadi na musamman domin magance wahalar mai da aka saba

Ba za ayi fama da matsalar man fetur a Disamban bana ba – Majalisar Tarayya

NNPC ta gamsar da Majalisa cewa ba za ayi wahalar mai ba
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa Majalisar Wakilai ta Tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa ana sa rai ba za ayi fama da matsanancin wahalar man fetur a karshen wannan shekarar kamar yadda aka saba kowane Watan Disamban a kasar ba.

Honarabul Joseph Akinlaja wanda shi ne Shugaban kwamitin harkar man fetur a Majalisar Wakilai na Najeriya ya bada wannan tabbaci a makon nan a lokacin da ‘Yan Majalisar su ka tashi su ka kai ziyara raiki zuwa Hedikwatar NNPC.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ki sa hannu a sabon kudirin tsarin zaben Najeriya

Kamfanin man na Kasa watau NNPC ya dauki wasu matakai wajen ganin man fetur bai yi karanci a kasar yayin da karshen shekara ta gabato ba. Ndu Ughamadu, wanda shi ke magana da yawun bakin kamfanin ya bayyana wannan.

Mista Ughamadu yace sun shirya tsaf domin ganin man fetur bai yanke ba a cikin ‘yan kwanakin nan. Kamfanin man Kasar ya hada-kai ne da Takwarorin sa domin ganin jama’a ba su yi fama da dan-karen wahalar man da aka saba ba

Kwanaki Shugaban kamfanin NNPC na kasa baki daya, Dr. Maikanti Baru, ya bayyana irin shirin da su ke yi wajen ganin an samu yalwar man fetur wanda zai kai ga masu shirin yin tafiye-tafiyen bikin Kirismeti da sabuwar shekara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel