Gaskiyar abinda yasa gwamnati ta wanke Saraki daga zargin fashin Offa

Gaskiyar abinda yasa gwamnati ta wanke Saraki daga zargin fashin Offa

Jaridar Vanguard ta ci karo da wasu shaidu dake dauke da dalilan da yasa ministan shari'a, Abubakar Malami, ya dage har sai da aka wanke shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, daga zargin hannunsu a fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu.

A takardun sakamakon binciken 'yan sanda da jaridar ta gani, rundunar 'yan sanda ta kasa samun hujjar dake nuna cewar Saraki da Ahmed sun ingiza 'yan ta'addar yin fashi a bankuna 9 a garin Offa. Kazalika sun samun hujjar cewar sun bayar da wata gudunmawa ga masu laifin ko kuma ganawa da su kafin su aikata fashin.

Rashin samun hujjar kai tsaye dake nuna akwai hannunsu a cikin fashin ne ya sa ofishin ministan shari'a zukewa daga shiga batun gurfanar da su Saraki, yana mai kafa hujja da cewar hurumin jiha ne tayi hakan, tunda an shirya tare da yin fashin ne a garin Offa, jihar Kwara, ba a birnin tarayya, Abuja, ba.

Gaskiyar abinda yasa gwamnati ta wanke Saraki daga zargin fashin Offa

Wadanda ake zargi da fashin Offa
Source: Depositphotos

Rahoton ya bayyana cewar Malami ya nusar da shugaban rundunar 'yan sanda kan illar gurfanar da su Saraki a kan zargin da babu hujjar da za a iya gabatar wa a gaban kotu.

DUBA WANNAN: An kulle mahaifina a kurkuku saboda ya yi kokarin hana ni zuwa makaranta - Atiku

Yanzu haka dai shugaban rundunar 'yan sanda ya bayar da umarnin kwace makamai da kudaden dake hannun 'yan fashin.

Kazalika an gurfanar da Alabi Olalekan, mai taimakawa gwamna Ahmed na musamman, bisa tuhumar sa da mallakar makami ba bisa ka'ida ba. An gurfanar da shi ne tare da 'yan fashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel