ASUU: Gwamnatin tarayya za ta gana da Malamai kan yajin aiki a ranar Litinin

ASUU: Gwamnatin tarayya za ta gana da Malamai kan yajin aiki a ranar Litinin

Za ku ji cewa gwamnatin tarayya a ranar Litinin 10 ga watan Dasumba, za ta gudanar da zaman sulhu tsakaninta da kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU dangane da ci gaban yajin aikinta da ya mamaye kasar nan.

Ministan kwadago da aikace-aikace, Dakta Chris Ngige, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin ma'aikatarsa, Mista Samuel Olowokere, a garin Abuja.

Dakta Ngige ya bayyana cewa, zaman tattaunawa domin cimma matsaya tsakanin kungiyar ASUU da ma'aikatar ilimi ta kasa za ya ci gaba da gudana da misalin karfe 4.00 na yammacin ranar Litinin a ma'aikatarsa ta Kwadago da aikace-aikace.

Ministan ya kuma bayyana bacin ransa dangane da furucin fitaccen Lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, da ya bayyana cewa hukuncin gwamnatin tarayya na rashin biyan albashi ga Malaman Jami'o'i ma su aiwatar da yajin aiki ya sabawa ka'ida.

Ministan Kwadago yayin zaman sulhu da kungiyar ASUU a ranar 4 ga watan Dasumba

Ministan Kwadago yayin zaman sulhu da kungiyar ASUU a ranar 4 ga watan Dasumba
Source: Depositphotos

Ko shakka ba bu a kwanaki kadan da suka gabata gwamnatin tarayya ta bayar da umarni na haramtawa Jami'o'in kasar nan biyan albashi ga Malamai ma su aiwatar da yajin aiki, inda ta kaddamar da hukuncin "ba bu biya idan ba bu aiki " a kansu.

Sai dai Ministan ya bayyana cewa, hukuncin wannan doka ta ba bu biya idan ba bu aiki karbabbiya ce karkashin ma'aikatar kwadago ko ina a fadin duniya.

KARANTA KUMA: Bayan wuya sai dadi: Al'ummar Najeriya za su sharbi romo a shugabancin Buhari karo na biyu - Akande

Shugaban kungiyar Daliban jami'o'in Najeriya, Mista Danielson Akpan, ya nemi gwamnatin tarayya da kuma kungiyar ASUU akan sulhuntawa domin dalibai su koma faggen fama na karatuttukan su.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, kungiyar ASUU a ranar 4 ga watan Nuwamba, ta afka yajin aiki gadan-gadan na sai Mama ta gani dangane da rashin cika alkawurran da gwamnatin tarayya da dauka na inganta harkokin karantawa tun a shekarar 2009 da ta gabata.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Jiragen dankaro kimanin 36 makare da tatattaccen man fetur da kuma kayan masarufi sun nufo Najeriya kamar yadda hukumar tashoshin jiragen ruwa ta kasa ta bayyana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel