2019: Bayan kayar da Buhari da zan yi harda ritaya zan yi masa – Atiku

2019: Bayan kayar da Buhari da zan yi harda ritaya zan yi masa – Atiku

Dan takarar sugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya ce a watan Fabrairun 2019, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi ritaya zuwa mahaifarsa Daura bayan zabe.

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ke martani ga furucin Adams Oshiomhole na ranar Laraba cewa zai sha kaye ba da wasa ba a 2019, yace yan Najeriya da suka sha fama da kangin wahalar gwamnatin Buhari ne za su yanke shawarar yadda makomar zaben zai kasance.

2019: Bayan kayar da Buhari da zan yi harda ritaya zan yi masa – Atiku

2019: Bayan kayar da Buhari da zan yi harda ritaya zan yi masa – Atiku
Source: Depositphotos

Da yake Magana tab akin hadiminsa, Paul Ibe, Atiku ya bukaci Oshiomhole da ya shirya ma makomarsa, mokamar Shugaba Buhari da kuma na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) anan gaba kadan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta amince da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar damokradiyya

Atiku ya ce yan Najeriya ba mahaukata bane, sun san wanda za su zaba duba ga matsalar rashin tsaro, rashin ayyuka da tarin bakin ciki da wahalar da suke ciki sanadiyar gwamnati mai mulki a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel