2019: Babban hadimin gwamnan Jigawa ya yi murabus, ya fita daga APC

2019: Babban hadimin gwamnan Jigawa ya yi murabus, ya fita daga APC

Babban hadimin gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru, kan harkokin gwamnatocin waje, Musdapher Kaloma, ya yi murabus daga kujerarsa kuma fita daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Musdapher Kaloma ya yi takaran kujeran majalisa ne karkashin jam’iyyar APC amma ya sha kasa.

Yayinda yake alanta murabus dinsa da sauka sheka a rana Alhamis ga manema labarai, ya tuhumci gwamna Badaru da laifin kama karya. Yace yawancin yan takaran da suka ci zaben fidda gwani an zabesu ne ba bisa ka’ida ba.

KU KARANTA: An damke matashi da laifin kisan mahaifinsa a Abuja

Mr Kaloma ya ce babu banbanci tsakanin jam’iyyar PDP da APC kan rashin demokradiyyan cikin gida.

“Na yi rijista da jam’iyyar SDP da sa ran cewa abubuwa za su gyaru kuma jama’a zasu fadi ra’ayinsu.”

“Abin takaici ne a ce shugabannin APC a jihar Jigawa sun dauki shugabanci matsayin hanyar samun arziki, ba bautawa jama’a ba, shi yasa jihar Jigawa batada wakilci mai inganci a majalisar dokokin tarayya.”

He said he met the governor one on one and even sent him an email on the grey areas that need corrections.

Barr Musdapher Kaloma ya kara da cewa ya tattauna da gwamna kuma ya tura masa sako kan gyare-gyaren da yakamata ayi amma bai amsa ba. Innama ya turo wasu su fada min cewa wanda muke neman kujeran tare ya girmeshi kuma mabiyinsa ne.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel