Yaki da cin hanci: Har yanzu da sauran aiki - Buhari

Yaki da cin hanci: Har yanzu da sauran aiki - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu ba’a gama cimma yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda gwamnatinsa ta so ba.

Da yake Magana a taron manyan masu bincikar kudi a Najeriya a Abuja, a ranar Talata, Buhari wanda ya samu wakilcin shugabar ma’aikata na tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita, ya bukaci manyan masu bincikar kudi a kasar da su bayar da gudunmawarsu wajen bayar da cikakken bayani kan hukumomin gwamnati domin a samu a zurfafa yaki da rashawa.

Yaki da cin hanci: Har yanzu da sauran aiki - Buhari

Yaki da cin hanci: Har yanzu da sauran aiki - Buhari
Source: Twitter

Buhari yace tun bayan hawarsu mulki, gwamnati mai ci ta samar da shiri daban-daban musamman a hukumar kudade domin ganin ta magance rashawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta amince da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar damokradiyya

Daga ciki wannan shiri akwai samar da asusun banki guda wato Treasury Single Account (TSA), wanda ya taimaka matuka wajen toshe kafofin sata a tsarin da kuma shirin Presidential Initiative on Continuous Audit (PICA).

Shugaban kasar ya kuma jadadda jajircewar gwamnatinsa wajen ganin ta cimma dukkanin alkawaran da ta daukarwa al’umman kasar, wanda a yanzu ake kan cimma nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel