Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da majalisa daga binciken badakalar dallan Ganduje

Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da majalisa daga binciken badakalar dallan Ganduje

Majalisar dokokin jiha ba ta da ikon bincike ko aika sammaci ga gwamna akan kowani shari’a na aikata laifi a cewar hukuncin babbar kotun Kano karkashin jagorancin Justis Ahmed Tijjani Badamasi.

A cewar Justis Badamasi karfin bincikar laifi ya ta’allaka ne a wuyan yan sanda, hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma hukumomi masu bincikar cin hanci kamar ICPC da sauransu.

Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da majalisa daga binciken badakalar dallan Ganduje

Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da majalisa daga binciken badakalar dallan Ganduje
Source: Depositphotos

Jaridar This Day ta ruwaito cewa Justis Badamasi ya ce majaisar dokoki na da ikon zartar da doka da sake duba dokokin da ken an amma ba wai binciken lamuran laifi ba.

Majalisar dokokin jihar Kano, shugaban kwamitin bincike na majalisar Baffa Baba Dangundi da atoni janar na jihar ne wadanda ake kara a lamarin.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Dino Melaye a kan sabuwar tuhuma

Idan za ku tuna, majalisar dokokin ta kafa kwamitin mutane bakwai don binciken wani rahoto da ke nuna bidiyon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan zargin cewa yana karan cin hanci daga hannun dan kwangila.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel