Za’ayi duk wacce za’ayi idan har aka yi magudi a zaben 2019 - Orubebe

Za’ayi duk wacce za’ayi idan har aka yi magudi a zaben 2019 - Orubebe

Tsohon ministan harkokin Niger Delta, Godsday Orubebe ya caccaki yadda aka gudanar da zaben 2015 sannan ya sha alwashin cewa ba za’a bari a yi magudi a zaben 2019 ba.

Orubebe wanda ya kasance dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya tada wani rigima a lokacn hada sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 lokacin da yayi zargi cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na waccan lokacin, Farfesa Attahiru Jega ya nuna son kai a yayinda yake yunkurin hargitsa shirin.

Za’ayi duk wacce za’ayi idan har aka yi magudi a zaben 2019 - Orubebe

Za’ayi duk wacce za’ayi idan har aka yi magudi a zaben 2019 - Orubebe
Source: UGC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce tayi nasarar lashe zaben a waccan lokacin.

Tsohon ministan, ya fada ma mujallar TELL na watan Nuwamba cewa ba za’a bari ayi magudin zabe kamar yadda aka yi a Ekiti ba a 2019.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta amince da samar da sabbin makarantun gaba da sakandare 6

A cewarsa, babu wanda ya iya ya take wa yan Najeriya hakkinsu na zabar shugaban kasarsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel