Malaman da El-Rufai ya fatattaka sun tabbatar da goyon bayansu ga Shehu Sani

Malaman da El-Rufai ya fatattaka sun tabbatar da goyon bayansu ga Shehu Sani

Wasu malaman firamari da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sallama daga aiki sun bayyana goyon bayansu ga takarar dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar da dattawa, Sanata Shehu Sani.

Malaman sun bayyana haka ne a yayin da suka kai ma Sanatan ziyara a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba 5 ga watan Disamba, inda suka yi alkawarin mara masa baya a kokarinsa na zarcewa akan kujerar tasa.

KU KARANTA: An kama mai kamawa: EFCC ta kama shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya da zambar naira biliyan 1.4

Malaman sun kara da cewa sun yanke shawarar goyon bayansa ne saboda shima ya bayyana damuwarsa da halin da suka shiga a lokacin da aka sallamesu daga aiki, da wannan ne yasa suka yanke shawarar rama masa biki.

Jagoran tawagan tsofaffin Malaman, Alice Ayuba ta bayyana cewa zasu tabbatar da sun mayar da Shehu Sani kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PRP ta hanyar yi masa ruwan kuri’a, kamar yadda majiyar Legit.com ta ruwaito.

“Mun zo ne da nufin bayyana godiyarmu ga Sanatan bisa kokarin goyon bayan daya bamu a lokacin da aka sallamemu daga aiki, ya jajirce wajen kwato mana hakkinmu, tare da fito da abokan aikinmu da aka kama a wancan lokaci, don haka zamu saka masa abinda yayi mana.” Inji shi.

Daya jawabi, Sanata Shehu San ya bayyana goyon bayan da tsofaffin Malaman suka bashi, sa’annan ya jaddada alhininsa ga sallamarsu da gwamnatin jahar Kaduna tayi, sa’annan ya tabbatar musu da cewa zai cigaba da kokarin kwato musu hakkinsu har sai an mayar dasu aikinsu.

“Abin mamaki ne ace bayan kun kwashe gomman shekaru kuna koyarwa wani yazo ya sallameku, bayan kuma kuna da kwarewa, amma rana daya wani yazo yace wai baku iya ba. ina tabbatar muku da cewa hanyar da aka bi wajen sallamarku ba bisa ka’ida bane.

“Ina tare daku a wannan gwagwarmayar da kuke yi, ku cigaba da gwagwarmaya, idan ma ba’a mayar daku yanzu ba, lokaci zai zo da lallai sai an mayar daku.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel