Toh fa! Gwamna El-Rufai ya bayyana matakin da zai dauka idan har ya fadi zaben 2019

Toh fa! Gwamna El-Rufai ya bayyana matakin da zai dauka idan har ya fadi zaben 2019

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa idan har an kayar da shi zaben 2019, toh ba zai jira har sai hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da sakamakon zaben ba zai rungumi kaddara, kuma ya amince da zaben al’ummar jahar Kaduna.

El-Rufai ya bayyana haka ne a yayin wani taron rattafa hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya da hukumar tabbatar da zaman lafiya ta jahar Kaduna ta shirya ma yan takarkaru a ranar Laraba 5 ga watan Disamba a garin Kaduna.

KU KARANTA:

A cewar gwamnan yana da wasu muhimman abubuwa daya kamata ya yi idan har bai samu nasara ba a yunkurinsa na neman tazarce akan mukamin gwamnan jahar Kaduna bayan zaben shekarar 2019 ba, kamar yadda majiyar Legit.com ta ruwaito.

Da wannan ne El-Rufai ya ja hankalin yan siyasa da mabiyansu game da furta muggan kalamai da zasu iya kai ga tunzura jama’a wajen tayar da rikici, hakanan ya yi gargadin jama’a su guji sukar kabila ko addinin juna musammana a kafafen sadarwar zamani.

Bugu da kari Gwamna El-Rufai ya yi kira ga yan siyasa dasu mayar da hankali wajen bayyana ma jama’a ayyukan da suka yi ko kuma suke burin yi idan har sun samu nasara, hakan ne kadai zai baiwa jama’a daman bambamce aya da tsakuwa.

“Magudin zaben da aka yi a shekarar 2011 ya janyo rikicin daya biyo bayan zaben wanda ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin jama’a a Kaduna, inda aka kiyasta an kashe sama da mutane dari takwas (800)” Inji gwamnan jahar Kaduna.

Amma ta sauya zani a zaben 2015, zaben da yawancin mutane suke ganin anyi shi bisa gaskiya gaskiya, musamman a Arewacin Najeriya, don haka ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika wuya tun kafin a sanar da sakamakon.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel