Hukumar NECA ta bayyana yadda za a kawo karshen rashin aiki a Najeriya

Hukumar NECA ta bayyana yadda za a kawo karshen rashin aiki a Najeriya

Kungiyar tuntube-tuntube da bayar shawarwari ga ma'aikata ta Najeriya watau NECA, Nigeria Employers' Consultative Association, ta bayyana mataki dangane yadda za a kawo karhen matsaloli da kalubalai da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Kungiyar a yayin shirye-shiryen rabuwa da babban jagoranta, Mista Olusegun Oshinowo, ta da'awar yadda sauya fasalin kasa za ya yi tasirin gaske wajen warware duk wata matsala gami da barazana da kasar nan ke fuskanta.

Cikin gabatar da jawabansa na bankwana, jagoran kungiyar da za ya ajiye aikinsa a karshen wannan wata na Dasumba, Mista Oshinowo ya bayyana cewa, matukar sauya fasalin kasar Najeriya tare da aiwatar da garambawul a cikinta bai tabbata ba, kalubalen da ta ke fuskanta ba za su taba kasancewa tarihi ba.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ya ruwaito, jagoran na NECA ya tabbatar da cewa, aiwatar da sauya fasalin kasa shine kadai tafarkin da za ya kawo karshen rashin tasaro,talauci, rashin aikin yi da sauraren ababe dake ciwa al'ummar kasar nan tuwo a kwarya.

Yadda Talauci ya yi katutu a Najeriya

Yadda Talauci ya yi katutu a Najeriya
Source: Depositphotos

Mista Oshinowo ya bayyana cewa, sauya fasalin kasa za ya yi tasirin gaske wajen bai wa jihohin kasar nan dama ta cin gashin kansu ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba wajen ingantawa da kuma habaka tattalin arziki a karsan kansu.

Yayin jaddada takaicinsa, Mista Oshinowo ya bayyana cewa kawo karshen rashawa a kasar nan ba za ya taka wata muhimmiyar rawa ba wajen tsarkake ta daga kalubalan da ta ke fuskata ballantana habakar tattalin arziki.

KARANTA KUMA: Makiyaya sun karbi fansar N2.2m kudin garkuwa a hannun ma'aikatan Kastam da NDLEA

Ba ya ga jihar Legas da kuma babban birnin kasar nan na tarayya, jagoran na NECA ya zayyana cewa, ba bu wata jiha da al'ummar ta ke ribatuwa ta fuskar tattalin arziki da kuma tsarkaka daga talauci ta hanyar samun abin dogaro da kai.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Majalisar dattawan Najeriya, ta bayar da sahalewartta na samar da wasu sabbin Makarantu 6 na gaba da Sakandire cikin wasu jihohi da ke fadin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel