2019: Bamu janyewa Atiku ba - GDPN

2019: Bamu janyewa Atiku ba - GDPN

Yan sa’o’i kadan bayan gamayyar kungiyar Coalition of United Political Parties (CUPP) ta sanar da tsayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin dan takararta, jam’iyyar Grassroots Development Party of Nigeria (GDPN), ta nisanta kanta daga wannan shiri.

A wata sanarwa daga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar GDPN, Dr. Davidson Isibor Akhimien, yace jam’iyyar bata da labara balle har ta marawa CUPP baya wajen yanke shawarar tsayar da Atiku.

2019: Bamu janyewa Atiku ba - GDPN

2019: Bamu janyewa Atiku ba - GDPN
Source: Facebook

CUPP ta kasance gamayyar manyan jam’iyyun siyasa 45 a kasar.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta amince da samar da sabbin makarantun gaba da sakandare 6

Wata sanarwa dauke da sa hannun Akhimien yace ya shiga alhini akan sanarwar CUPP, cewa a lokacin da ake taron tsayar da Atiku a Abuja shi yana Lagas, inda ya kara da cewa jam’iyyar ma bata cikin wannan shirin ko kadan.

Ya kuma sha alwashin cewa ba zai watsar da kudirinsa na son kawo gyara a kasar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel