Ba mu bukatan Okorocha da Amosun - Oshiomole

Ba mu bukatan Okorocha da Amosun - Oshiomole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole, ya ce shaharar da APC ke da shi a jihar Imo da Osun ya isa su samu nasara a 2019 duk adawa da gwamnonin jihar ke nunawa.

Ya siffanta gwamnonin a matsayin mutane da suka manta tarihi da wuri saboda sun dade suna takaran zabe suna fadi kafin suka samu a jam’iyyar APC.

Oshiomole ya bayyana hakan ne bayan karban bakoncin matan jam’iyyar APC shiyar jihar Edo yayinda suka kawo masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake Abuja.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha; gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari; da gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun; sun kasance cikin takun tsaka da shugaban jam’iyyar kan zaben fidda gwani.

A yanzu haka, wadanda gwamnonin ke so sun fita daga jam’iyyar APC saboda Oshiomole ya hanasu tikitin jam’iyyar karfi da yaji.

Oshiomole yace: “Wadanda sukayi tunanin rana goben jam’iyyarmu na hannunsu sunada saurin mantuwa ne. wadannan mutanen na daukan kansu wani abu, sun manta cewa a baya suna takara kuma suna fadi har lokacin da suka bar jam’iyyunsu suka dawo wajenmu.”

“Ko kai babban mutum ne ko karamin mutum ne, dokoki basu nuna banbanci. Shahararmu a Imo da Ogun ya kara girma yanzu.”

Gwamnonin jihar Ogun da Imo sun bayyana cewa ba zasu goyi bayan yan takaran gwamnan APC a jihohinsu ba saboda ba’a baiwa wadanda suke so tikiti ba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel