Wata sabuwa: Magu ya karayata masu cewa ya halarci taron nuna goyon baya ga Buhari

Wata sabuwa: Magu ya karayata masu cewa ya halarci taron nuna goyon baya ga Buhari

- Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC ya karyata masu yayata cewa ya halarci wani taro na nuna goyon baya ga shugaban kasa Buhari

- A cewar EFCC, shugaban hukumar na tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe, Abuja, a hanyarsa ta zuwa Legas, a lokacin da aka ce an gudanar da taron

- Hukumar ta ce ta tuntubi lauyoyinta, kuma suna kan nazari kan wannan labari da jaridar Premium Times ta wallafa, don daukar matakin da ya dace

Ibrahim Magu, shugaban hukumar da ke yaki da masu yiwa dukiyar al'uma zagon kasa tare da masu cin hanci da rashawa, (EFCC) ya karyata masu yayata cewa ya halarci wani taro na nuna goyon baya ga shugaban kasa Buhari, wanda aka ce an gudanar a Nicon Luxury Hotel, Abuja.

Cikin wata sanarwa daga kakakin hukumar INEC, Tony Orilade ya ce a lokacin da akayi ikirarin an gudanar da taron, shugaban hukumar EFCC na tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe, Abuja, a hanyarsa ta zuwa Legas, inda ya gana da shuwagabannin kafofin watsa labarai.

"Hukumar EFCC ta samu rahotanni kan wani labari da kafar watsa labarai ta Premium Times ta wallafa a shafinta na yanar gizo a ranar 5 ga watan Disamba, 2018, mai taken: "EFCC Chairman, Ibrahim Magu, attends Buhari re-election gathering”. (Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya halarci taron nuna goyon bayan tazarcen Buhari), wanda kuma karyace tsagoranta don cimma wata manufa.

KARANTA WANNAN: Akwai dalilin da ya sa Buhari bai kamata ya sa hannu a dokar zabe ta 2018 ba

Wata sabuwa: Magu ya karayata masu cewa ya halarci taron nuna goyon baya ga Buhari

Wata sabuwa: Magu ya karayata masu cewa ya halarci taron nuna goyon baya ga Buhari
Source: Depositphotos

"A cewar labarin, wanda Samuel Ogundipe ya wallafa a shafin jaridar, cewar Magu ya halarci taron ne don bayar da hanyoyin yadda za a gudanar da yakin zaben tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

"Taron wanda aka ce an gudanar a ranar Talata a otel din Nicon Luxury, Abuja, ya shafi wata kungiya ta tuntu ba don 'yan siyasar jam'iyyar APC. Kwamitin kungiyoyi masu goyon bayan Buhari na kasa, ya shirya taron ga masu mubayi'a ga shugaban kasa Buhari," a cewar rahoton.

"Sai dai gaskiyar magana shine, Mr Ibrahim Magu bai halarci wannan taro ba. Da misalin karfe 8:59 na safiyar Talata, 4 ga watan Disamba, 2018, shugaban hukumar EFCC na harabar tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe, Abuja don zuwa jihar Legas inda ya tattauna da shuwagabannin kafafen watsa labarai.

"Muna so mu tabbatar da cewa shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Mustafa Magu, baya cikin wata jam'iyyar siyasa kuma ko kadan bai da hannu a harkokkin jam'iyyar APC. Yana gudanar da aikinsa ne kawai bisa kwarewa, kuma zai ci gaba da aikinsa ba tare da shiga harkokin siyasa ba.

"Zuwa yanzu, mun tuntubi lauyoyinmu, kuma suna kan nazari kan wannan labari da jaridar Premium Times ta wallafa, don daukar matakin da ya dace," a cewar Orilade.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel