Buhari bai da niyyar sa hannu a sabon kudirin tsarin zabe – Inji CUPP

Buhari bai da niyyar sa hannu a sabon kudirin tsarin zabe – Inji CUPP

- Jam’iyyun adawa sun hurowa Shugaban kasa Buhari daga dawowan sa Najeriya

- CUPP tace Shugaban kasar bai da niyyar sa hannu a sabon kudirin tsarin zabe

Mun ji cewa Kungiyar CUPP ta hadakar Jam’iyyun adawan hamayya a Najeriya ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari na kokarin yin mursisi da sa-hannu a sabon kudirin tsarin zabe na kasar da aka aika masa.

Buhari bai da niyyar sa hannu a sabon kudirin tsarin zabe – Inji CUPP

'Yan adawa sun zargi Buhari da niyyar amfani da 'Yan Sanda a zaben 2019
Source: Depositphotos

CUPP ta fitar da jawabi ta bakin Mai magana da yawun ta watau Ikenga Ugochinyere a cikin makon nan. Ikenga Ugochinyere yace da gan-gan da Shugaban kasar ya ki sa hannu a kan kudirin tsarin zabe na 2018 har wa yanzu.

Kungiyar ta Jam’iyyun hamayyan Kasar ta bayyana cewa tayi mamakin yadda Shugaba Buhari yake kokarin murde zaben 2019 duk da cewa yana ikirarin an dade ana murde masa zabe lokacin yana adawa da Gwamnatin Kasar.

Jam’iyyun hamayyar a karkashin reshen CUPP sun nuna cewa akwai kishin-kishin din cewa Buhari ba zai amince da sabon dokar zaben da ake kokarin dabakkawa ba. Wannan ne dai karo na biyu da Shugaban yayi watsi da kudirin.

KU KARANTA: Atiku da Obasanjo za su dauki kashin su a hannun APC inji Oshiomhole

A baya, Shugaba Buhari yayi ta wala-wala har wa’adin sa hannu ya shude inda Kungiyar ta CUPP ta hurowa Shugaban Kasar wuta yayi maza ya sa hannu a sabon kudirin tsarin zaben wannan karo domin ganin an yi zaben adalci a badi.

CUPP tace Gwamnatin APC na shirin murde zabuka a wasu Jihohi 10 wanda su ka hada da Benuwai. Sauran Jihohin da za a nemi a murde zaben su ta hanyar amfani da Jami’an tsaro sun hada da Ribas da kuma Jihar Edo inji Kungiyar.

Kungiyar ta CUPP tace idan har da gaske ba wani bane ke dauke da fuskar Shugaban kasar daga wata Kasa kamar yadda ake ta rayawa, Buhari yayi na’am da wannan kudiri da aka kawo gaban sa tun-tuni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel