Majalisar dattawa ta amince da samar da sabbin makarantun gaba da sakandare 6

Majalisar dattawa ta amince da samar da sabbin makarantun gaba da sakandare 6

Majalisar dattawa a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba ta gabatar da dokoki shida dake neman a samar da manyan makarantun gaba da sakandare na tarayya a yankuna daban-daban a kasar.

Makarantun sune polytechnics guda hudu, kwalejin ilimi guda da kuma jami’ar fasaha guda daya.

Za’a gina polytechnics din ne a Mpu, jihar Enugu; Kwale a Delta; Kaltungo a jihar Gombe, da kuma Adikpo a Benue.

Majalisar dattawa ta amince da samar da sabbin makarantun gaba da sakandare 6

Majalisar dattawa ta amince da samar da sabbin makarantun gaba da sakandare 6
Source: Depositphotos

A dayan bangaren, jami’ar wanda aka fi sani da City University of Technology zai kasance a Auchi da ke Edo, yayinda kwalejin ilimin zai kasance a Omuo-Ekiti a Ekiti, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

KU KARANTA KUMA: 2019: Karshen mulkin Shugaba Buhari ya karaso - Inji Jam'iyyar PDP

Gabatar da dokokin a gaban majalisa ya biyo bayan duba rahotanninda kwamiti makarantun gaba da sakandare ta gabatar ta hannun shugabanta, Jibrin Barau.

Da yake gabatarwa, Barau yace kasar na da karanci makarantun gaba da sakandare don haka akwai bukatar a cimma manufofin ilimi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel